Da Duminsa: Saudiyya ta sanar da ranar bude kofa kowa ya zo Umrah

Da Duminsa: Saudiyya ta sanar da ranar bude kofa kowa ya zo Umrah

 • Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da ranar da za a ci gaba da Umrah na kasa da kasa
 • Ta kuma bayyana cewa, akwai kasashen da dole su cika wasu ka'idoji na annobar Korona
 • Legit.ng Hausa ta tattaro daga wata sanarwar da ta bayyana abubuwan da ake bukata na Umrah

Kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar cewa, ta amince da a ci gaba da ayyukan Umrah na kasa da kasa daga ranar 1 ga watan Muharram.

Sanarwar, wacce Legit.ng Hausa ta samo a shafin Facebook na Haramain Sharifain, ta bayyana tsarukan da da gwamnatin kasar ta fitar ga kasashen da za su zo ayyukan na Umrah.

Sanarwar ta ce, dukkan kasashen duniya za su iya turo jiragensu kai tsaye, yayin da kasar ta ware wasu kasashe tara (9) da basu amince su shigo kai tsaye ba tare da kebewar Korona ba na kwanaki 14.

Da Duminsa: Saudiyya ta sanar da ranar da za a fara Umrah na kasashen duniya
Sanarwar Saudiyya | Hoto: Haramain Sharifain
Asali: UGC

Kasashe 9 da Saudiyya ta ware cewa dole su yi kulle na Korona

Kara karanta wannan

FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi

 1. India
 2. Pakistan
 3. Indonesia
 4. Egypt
 5. Turkey
 6. Argentina
 7. Brazil
 8. South Africa
 9. Lebanon

Hakazalika ana bukatar dukkan mai zuwa Umrah da ya tabbatar cewa, yayi allurar rigakafin Korona AstraZeneca, Pfizer, Mordena ko kuma J&J. Sannan dole ya zama mai ziyarar Umrah ya zama daga shekaru 18 ya yi samu.

Kasar Larabawa ta kirkiri manhajar soyayya don hada aure daidai da tsarin Muslunci

A wani labarin, mahukunta a kasar Iran sun kaddamar da wata manhaja ta soyayya wadda suka ce nufinta shi ne ta saukake neman aure bisa tsarin addinin Musulunci, BBC Hausa ta ruwaito.

Hukumar yada manufofin addinin Musulunci ta kasar ce ta kirkiro manhajar mai suna Hamdam wadda ke nufin aboki ko abokiyar zama, AlJazeera ta ruwaito makamancin haka.

Manhajar tana amfani da basirar komfuta wajen hada wadanda suke son su yi aure, kodayake mata daya kacal aka amince wa namiji ya aura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel