Rahoto: Jerin taurarin Kannywood 5 da suka taba zaman aure kafin fara harkar fim

Rahoto: Jerin taurarin Kannywood 5 da suka taba zaman aure kafin fara harkar fim

Harkar fina-finan Hausa, musamman a arewacin Najeriya harkace da take dauke da fitattun jarumai masu gwazo; maza da mata

Mabiya shafukan sada zumunta kan yawaita tambayar yadda rayuwar wadannan jarumai take, da kuma asalin inda suka fito

Wani rahoto da Legit.ng Hausa ta samo ya binciko wasu jarumai mata da suka tsunduma harkar fim bayan rabuwa da mazajensu

Akwai wasu jerin jarumai mata da sai bayan ballewar aurensu tauraruwarsu ta fara haskawa a masanaantar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Wasu na ganin cewar da zarar jaruma ta yi aure shikenan tauraronta ya daina haske ko an daina damawa da ita a masana’antar, amma a wani duba da aka yi a kan wasu jarumai biyar da suka shahara bayan rabuwa da mazajensu, Aminiya ta rfuwaito.

1.Jamila Umar Nagudu

Jaruma Jamila Nagudu, ta yi fice matuka a harkar fina-finan Kannywood, inda ta yi fina-finai da dama, sai dai, kafin shigarta masana'antar Kannywood, ta taba yin aure har ma da yaro guda daya.

Read also

Allah Ya Isa Ban Yafe Ba, Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Yi Martani Ga Masu Sukarta

Jamila ta bayyana a fina-finai da dama amma wanda ta fi taka muhimmiyar rawa a ciki kuma ya zama shi ne silar haskawarta shi ne fim din ‘Jamila da Jamilu’, inda ta fito tare da jarumi Ibrahim Maishinku a shekarar 2008.

Jerin taurarin Kannywood 5 da suka shahara bayan mutuwar aurensu
Jamila Nagudu da Danta | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

2. Hafsat Idris (Barauniya)

Hafsat Idris ta yi fice a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, bayan rugujewar aurenta da tsohon mijinta Alhaji Kabir, wanda suka haifi yara biyar har da shi.

Jarumar ta fara fitowa a cikin fim din ‘Barauniya’ wanda da shi ne wasu ’yan kallo ke mata lakabi dashi; Hafsat Barauniya.

Tuni Hafsat ta yi fice ta zama daya daga cikin manyan jarumai mata da ake ji dasu kuma mai shirya fina-finai da ake damawa da su a masana'antar Kannywood.

Jerin taurarin Kannywood 5 da suka shahara bayan mutuwar aurensu
Hafsat Idris Barauniya | Hoto: desertherald.com
Source: UGC

3.Umma Shehu

Umma Shehu na daya daga cikin jarumai mata fitattu kuma shahararru a masana'antar Kannywood kana wacce take haskawa a duniyar fina-finan Hausa.

Read also

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Ita ma, kafin shigarta masana’antar Kannywood, jarumar ta taba zaman aure, inda ta ke da yara mata har guda biyu.

Ta fito a fina-finai irinsu Mijin Badariyya, Bakon Yanayi, Amaryar Kauye, Burin So, da kuma shiri mai dogon zango na Gidan Badamasi.

Jerin taurarin Kannywood 5 da suka shahara bayan mutuwar aurensu
Umma Shehu | Hoto: desertherald.com
Source: UGC

4. Maimuna Garba (Momee Gombe)

Bayan rabuwarta da mawaki Adamu Fasaha, Maimuna Garba, wacce aka fi sani da Momee Gombe ta tsunduma harkar wakoki a masana’antar Kannywood kuma ta yi fice a cikin wakar ‘Jaruma’ ta mawaki Hamisu Breaker.

Bayan tauraronta ya haska a fagen waka, jarumar ta fara fitowa a cikin fina-finai kamar su Zainabu Abu, Manyan Mata, Gidan Danja da sauransu.

Jerin taurarin Kannywood 5 da suka shahara bayan mutuwar aurensu
Momee Gombe | Hoto: naijanetworth.com.ng
Source: UGC

5. Aisha Najamu

Binciken na Aminiya ya gano jarumar ta taba zaman aure har ma da yara biyu kafin ta shigo masana’antar Kannywood.

Jarumar ta yi fice a cikin shirin fim mai dogon zango na Izzar So wanda a cikinsa ne ta nuna bajinta har tauraronta ya haska, aka fara damawa da ita a cikin masana’antar Kannywood.

Read also

Hoton Matar Da Ta Haɗa Baki Da Mijinta Don Ƙaryar Garkuwa Da Ita a Jihar Niger

Jerin taurarin Kannywood 5 da suka shahara bayan mutuwar aurensu
Aisha Najamu | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Wadannan su ne jerin jarumai mata biyar fitattu da tauraruwarsu ta fara haskawa a Kannywood bayan fitowa daga gidajen aurensu.

Auren Yusuf Buhari: An kaddamar kwamitin mutane sama da 100 don kula da daurin aure

A wani labarin, An kammala shirye-shiryen daura auren Yusuf, dan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), tare da diyar Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Ado-Bayero, a ranar 20 ga watan Agusta, Reuben Abati ya ruwaito.

Mai magana da yawun masarautar Bichi, Lurwanu Malikawa, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado-Bayero, ya kaddamar da wani kwamiti na mutum 145 don saukaka bikin auren ba tare da matsala ba.

Sanarwar ta yi nuni da cewa Hakimin Bagwai, Nura Ahmad (Madakin Bichi) ne zai jagoranci kwamitin, tare da Abba Waziri (Falakin Bichi), a matsayin sakatare.

Source: Legit.ng

Online view pixel