Babban Limami ya ziyarci coci kuma ya yi addu’a tare da kiristoci, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Babban Limami ya ziyarci coci kuma ya yi addu’a tare da kiristoci, bidiyon ya haddasa cece-kuce

  • Wani bidiyo na wani babban limami yana addu’a tare da mabiya addinin kirista a coci a yankin Ikorodu ya sanyaya zukata a shafin soshiyal midiya
  • A cikin bidiyon, malamin musuluncin ya yi addu’a daidai da koyarwar imaninsa da na kirista inda mambobin cocin suka amsa
  • Mutane da dama a shafin soshiyal midiya sun ce haka ya kamata abubuwa su dunga kasancewa tsakanin Musulmi da kirista

Wani biyu bidiyo na wani babban limami yana addu’a tare da mabiya kirista a coci a yankin Ikorodu da ke jihar Lagas ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a soshiyal midiya.

A cikin bidiyon wanda shafin @instablog9ja ya wallafa a Instagram, limamin ya yi addu’a na Musulunci da kirista inda taron jama’an suka amsa.

Babban Limami ya ziyarci coci kuma yayi addu’a tare da kiristoci, bidiyon ya haddasa cece-kuce
Babban Limami ya yi addu’a tare da kiristoci Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Ya ce:

“Mu yi godiya ga Allah. Godiya ga Ubangiji. Wani ya yi ihun Alleluia. Wani ya ce Amin. Addu’anmu karbabbe ne, Za mu cika da farin ciki. Girbin wannan shekarar ba zai zama na karashe a garemu ba. Godiya ga Ubangiji. Wani ya ce Amin.”

Kara karanta wannan

Mai 'Car Wash' ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci

Malamin kiristan yana a bayan takwaransa na Musulunci a duk wannan tsawon lokaci kuma yana ta addu’a yayin da addu’an ke gudana.

Abun ya birge mutane da yawa

@glowryhaa ya ce:

"Addini zaman lafiya ne."

@thriftsterclothing yayi sharhi:

"Soyayya daya ... kamar yadda ya kamata."

@ hope_benjamin29 ya rubuta:

"Mmmm abubuwa suna canzawa."

Shahararren fasto ya yi bikin Sallah tare da Musulmai a Masallaci

A wani labarin, babban fasto, Reverend Father Peter Ayanbadejo ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan sada zumunta bayan ya yi bikin Eid-el-Kabir tare da Musulmai a wani babban masallaci a karamar hukumar Ogun Waterside da ke jihar Ogun.

Shafin Facebook na The Partner Newspaper, Ijebu-Ode-Ode Diocese ne ya wallafa hotunan malamin na addinin kirista tare da takwarorinsa Musulmai.

Reverend Father Ayanbadejo ya kasance shugaban Ogbere Catholic Deanery.

Asali: Legit.ng

Online view pixel