Shahararren fasto ya yi bikin Sallah tare da Musulmai a Masallaci, kyawawan hotuna sun janyo cece-kuce
- A kokarin kara dankon zumunci tsakanin addinai, Reverend Father Peter Ayanbadejo ya yi bikin Eid-el-Kabir tare da Musulmai a wani babban masallacin jihar Ogun
- An wallafa hotunan malamin addinin kiristan da takwarorinsa na musulmai a shafukan sada zumunta kuma abun ya burge 'yan Najeriya
- A tuna cewa daukacin al’umman musulmai a kasar sun yi bikin Eid-el-Kabir wanda aka fi sani da babban Sallah a ranar Talata, 20 ga Yuli
Babban fasto, Reverend Father Peter Ayanbadejo ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan sada zumunta bayan ya yi bikin Eid-el-Kabir tare da Musulmai a wani babban masallaci a karamar hukumar Ogun Waterside da ke jihar Ogun.
Shafin Facebook na The Partner Newspaper, Ijebu-Ode-Ode Diocese ne ya wallafa hotunan malamin na addinin kirista tare da takwarorinsa Musulmai.

Asali: Facebook
Reverend Father Ayanbadejo ya kasance shugaban Ogbere Catholic Deanery.
A wasu daga cikin hotunan, ana iya ganin faston zaune a kan tabarma a cikin masallacin. Hakanan za'a iya ganin sa yana ɗaukar hoto tare da wasu al’umman musulmai.
Lamarin ya burge mutane da dama
Johnpaul Orebanjo ya ce:
"Jagora mai kyau Allah ya karbi aikinka amin ta wurin shugabanmu Yesu."
Godwin Sunday Alphonsus ya yi sharhi:
"Kyakkyawan jagora wannan ita ce hanya daya da za a sanar da su cewa Allah daya ne kuma mu 'ya'yansa ne."
Ademiloye Odunayo Mary ta rubuta:
"Mun gode shugaba."
A wani labari na daban, mun ji cewa Masarautar Daura ta nada wa dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf, sarautar Talban Daura.
Babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da labarin nadin da aka yiwa Yusuf a yau Talata, 20 ga watan Yuli a wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.
An nada masa sarautar ne tare da Musa Daura, wanda yanzu shine Dan Madamin Daura.
Asali: Legit.ng