Yanzu-yanzu: Jami'an Jamhuriyar Benin na yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi

Yanzu-yanzu: Jami'an Jamhuriyar Benin na yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi

  • Dan gwagwarmayar nan mai fafutukar kare ƙasar Yarbawa, Sunday Igboho, na gab da sanin makomar shi
  • An tattaro cewa jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin a Cotonou na yi wa Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi
  • Bayan tambayoyin, za a kai dan fafutukar Cour d'Appel domin sauraron kararsa

Rahotannin da ke zuwa mana sun nuna cewa jami’an gwamnatin kasar Benin sun fara yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi a Cotonou.

Wata majiyar shari'a da ta yi magana da BBC Pidgin ba tare da bayyana asalinta ba ta tabbatar da hakan a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli.

Ana sa ran dan gwagwarmayar Yarbawan zai wuce zuwa Cour d’Appel da ke Cotonou inda alkali zai yi shari’arsa.

Yanzu-yanzu: Jami'an Jamhuriyar Benin na yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi
Idan har aka tabbatar da cewa bai aikata ko daya daga cikin laifukan da ake zarginsa da shi ba a Jamhuriyar Benin, mai gabatar da kara zai tantance matakin da za a dauka na gaba. Hoto: Sunday Igboho
Asali: Instagram

Daga wani bangare na sauraren karar, kotun za ta yi muhawara kan sammacin kamun Igboho na kasa da kasa tare da aiwatar da shi idan har aka gano tana bisa hanya.

Kara karanta wannan

Da Dumisa: Kotu a kasar waje ta sa ranar yanke shawarin mika Sunday Igboho Najeriya

Yiwuwar wanke Igboho

Sai dai kuma, jaridar The Nation ta tattaro cewa idan har aka tabbatar da cewa mai fafutukar bai aikata ko daya daga cikin laifukan da ake zarginsa da shi ba a Jamhuriyar Benin, mai gabatar da kara zai tantance matakin da za a dauka na gaba.

Kotu a kasar waje ta sa ranar yanke shawarin mika Sunday Igboho Najeriya

A baaya mun ji cewa wata kotu a Jamhuriyar Benin ta tsayar da ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, don fara sauraron shari’ar da ake yi wa Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa.

Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki ne ya bayyana shirin sauraren karar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, in ji PM News.

Dan awaren Yarbawan, wanda har yanzu ke hannun Brigade criminelle a Cotonou zai san makomarsa yayin sauraron karar, jaridar The Nation ta kara da cewa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng