Nyesom Wike ya nemi alfarma wajen Gwamnatin Tarayya, Buhari ya biya masa bukatarsa
- Gwamna Nyesom Wike ya ce za a gina makarantar zama Lauya a jihar Ribas
- Nyesom Wike ya roki Gwamnatin Tarayya ta gina masa wannan makaranta
- Gwamnatin Tarayya ta dauki wannan matakin bayan Gwamnan ya kai kuka
Mai girma Gwamna Nyesom Wike na Ribas, ya yabi matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na gina makarantar koyon aikin shari’a a jiharsa.
The Guardian ta ce Nyesom Wike ya na ganin gina wannan makaranta a Ribas duk da irin sukar da yake yi wa gwamnatin tarayya, abin a yaba ne.
Da yake magana a wajen kaddamar da fara wannan aiki a garin Rumueme a karamar hukumar Obio-Akpor, Wike ya alwashin za a karasa aikin.
KU KARANTA: Duk da ANPP ta na da Gwamnoni a 2007, Gwamna 1 ya iya taimakon Buhari
Ribas ta samu makarantar koyon aikin shari'a
Gwamna Nyesom Wike ya ce gwamnatinsa za ta dage domin ganin an gina wajen koyon ilmin shari’a a jihar Ribas wanda babu irinsa a ko ina.
Ganin gwamnatin tarayya ta amince da rokonsa, an soma ginin wannan sabuwar makaranta, Wike ya ce mutanen jihar Ribas za su samu abin yi.
“Ina mai tabbacin cewa kowa a jihar Ribas zai san cewa matakin kafa makarantar koyon ilmin shari’a a garin Fatakwal ya na da muhimmanci.”
“Ba wai kawai zai taimaka wajen ba wadanda suka karanci ilmin shari’a damar zuwa makaranta ba, zai bunkasa tattalin arziki, za a samu ayyukan yi.”
KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta ba Manoma N6.15bn a bana
AGF ya kaddamar da ginin wannan makaranta
Shugaban majalisar makarantun ilmin shari’a, Nnaemeka Ngige (SAN), ya wakilci Ministan shari’a a wajen bikin kaddamar da ginin makarantar.
A madadin Abubakar Malami, Nnaemeka Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yarda ta gina makarantar ne bayan gwamnan ya nemi alfarma.
Ngige yake cewa duk idan za a kara gina irin wannan makaranta, dole ayi koyi da jihar Ribas.
Kungiyar Sarakiyya 2023 ta fito da korayen huluna a matsayin alama, suna harin kujerar Shugaban kasa. Mun samu wannan labari ne a farkon nan.
Kungiyar ta na goyon bayan Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ya shiga Aso Rock Villa.
Asali: Legit.ng