Alkali ya bada dama EFCC ta karbe kudi da kadarorin na-kusa da tsohuwar Minista, Diezani

Alkali ya bada dama EFCC ta karbe kudi da kadarorin na-kusa da tsohuwar Minista, Diezani

  • Lauyoyin Hukumar EFCC sun sake koma wa wajen Alkalli da Jide Omokore
  • Ana zargin hadimin tsohuwar Ministar man tarayyan da satar Dala biliyan 1.6
  • Za a sake karbe kudi da gidajen Omokore zuwa lokacin da za a gama bincike

Kotun daukaka kara da ke garin Abuja ya sake ba EFCC damar karbe wasu kadarorin hadimin tsohuwar Ministan mai, Diezani Alison-Madueke, Jide Omokore.

Za a rufe asusun barki, a karbe gidajen Jide Omokore

Jaridar The Nation ta ce kotu ta amince wa hukumar EFCC ta rufe asusun bankin Jide Omokore.

Jide Omokore wanda ya yi aiki tare da Diezani Alison-Madueke a lokacin ta na Ministar harkar mai, zai rasa dukiyoyi da gidajensa, akalla kafin a kammala shari’a.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta sallami Bala Usman daga NPA – Buhari

Rahoton ya ce akwai makudan kudi a cikin asusun wannan mutumi da ake tuhuma da sata, sannan ya mallaki manyan gidaje a Najeriya da kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Yadda wasikar Jakadan Najeriya, Tukur Buratai ta taimaka wajen cafke Igboho a kasar Benin

Alkali Moore Adumein ya jagoranci shari’ar da aka yi da tare da wasu Alkalai biyu, suka yi fatali da hukuncin da Alkalin kotun tarayya, Ahmed Mohammed ya yi.

Da yake zartar da hukunci a shari’a mai lamba CA/ABJ/CV/994/2020, Alkali Peter Ige, ya tabbatar da rokon da lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya ke yi a gaban kotu.

Peter Ige ya yi watsi da ikirarin Omokore na cewa taba masa dukiya ya ci karo da hakkinsa na ‘dan kasa, Alkali ya ce lauyan Omokore bai shigar da karar da kyau ba.

Diezani Alison-Madueke
Tsohuwar Minista, Diezani Alison-Madueke Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Yajin-aiki ya jawo cikas a shari'ar Diezani Alison-Madueke

Ige yake cewa ba zai yiwu Omokore da kamfaninsa na Energy Property, su tsaya a kotu da lauya daya ba, ya ce ya kamata kowane ya samu lauya dabam da zai kare shi.

Tarihin shari'ar Jide Omokore da EFCC

A wata shari’a mai lamba FHC/ABJ/CR/121/2016 da aka yi a 2016, kotu ta yarda EFCC ta rufe asusun Omokore bisa zargin sa da ake yi da satar fam Dala biliyan 1.6.

Kara karanta wannan

Abduljabbar: Wasu fitattun Malaman addini da suka shiga hannun Jami'an tsaro a gida da waje

Daga baya sai Alkali ya yi watsi da wannan shari’a, wanda hakan ya sa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta daukaka karar.

Sauran wadanda ake kara tare da Jide Omokore sun hada da; Victor Briggs, da Abiye Membere.

A watan nan ne aka ji cewa EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamna Mukhtar Ramalan Yero a gaban Alkali mai shari'a M.G Umar a babban kotun tarayya na Kaduna.

EFCC tana binciken Yero da wasu da zargin raba kudi har naira miliyan dari bakwai wanda tsohuwar ministan mai, Diezani Alison-Madueke ta raba a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel