Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Musulmai, sun yi sallar idi a Kaduna
Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi limancin sallar idi a garin Kaduna
Khalfin Tijjaniyan ya jagoranci sallar a filin idi na Murtala Muhammad a jiya
Muhammadu Sanusi II ya yi huduba a kan zaman lafiya da kwanciyar hankali
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi sallar idi a garin Kaduna, inda har ya jagoranci al’ummar musulmai su ka gudanar da sallah.
Malam Muhammadu Sanusi II shi ne ya yi limancin sallar wannan idi a filin idi na Murtala Mohammed da ke garin Kaduna jiya da safe.
Kusan duka musulman Duniya sun yi sallar babbar idi ne a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, 2021.
KU KARANTA: Mai dakin tsohon Sarkin Kano Sanusi II ta yi digiri a Turai
Dinbin mutane sun yi sallah a wannan fili da jagoran na darikar Tijjaniya ya jagoranta. Sanusi II ne ya yi limanci a wannan fili a karamar sallah.
Eid-el-Kabir: Bidiyo ya nuna Buhari yana tafiya zuwa filin Idi a Daura yayin daama'a ke taya shi murna
Gwamna ya yi sallah a bayan Muhammadu Sanusi II
Kamar yadda The Nation ta fitar da rahoto, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya na cikin wadanda suka yi sallah a bayan Sanusi II.
Haka zalika Sanatan da ke wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani, ya dawo gida domin ya yi bikin idi, kuma ya yi sallah a filin.
Muhammadu Sanusi II ya yi huduba a kan zaman lafiya
Da yake huduba bayan sallar, Sanusi II ya yi kira ga mutanen Najeriya su cigaba da zama lafiya, ba tare da nuna banbancin addini da kabilanci ba.
KU KARANTA: Goron sallah: Abubuwan da ya dace a sani game da sallar idi
Rahoton ya nuna cewa tsohon Sarkin na Kano da aka tsige a 2020 ya fadakar da al’ummar musulmai kan zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Da yake jawabinsa, mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa an baza jami’an tsaro domin a bankado miyagu a Kaduna.
Gwamna El-Rufai ya ce jami’an tsaro za su yi kokari domin su kawo zaman lafiya a jihar Kaduna.
A baya kun ji Malam Muhammadu Sanusi II ya jinjinawa Malaman da suka kalubalanci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma da'awar da yake kai.
Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga al'umma su bar doka ta yi aiki, sannan ya roki hukuma ta dauki matakin da ya dace a kan wannan shehin malami.
Asali: Legit.ng