Sarkin Daura ya ba Yusuf Buhari sarautar da ya taba ba Shugaban kasa a bikin idin 2019

Sarkin Daura ya ba Yusuf Buhari sarautar da ya taba ba Shugaban kasa a bikin idin 2019

  • Sarkin Daura Farouk Umar Farouk ya ba Yusuf Buhari sarautar ‘Talba’
  • A bikin sallar nan ne aka ba ‘Dan shugaban kasar wannan babbar sarauta
  • Amma Sarkin ya taba ba Shugaban kasar Guinea wannan sarauta a 2019

Yusuf Buhari ya zama sabon Talban Daura

A bikin karamar sallar bana ne Yusuf Muhammadu Buhari ya zama Talban Daura. Garba Shehu ya ce Farouk Umar Farouk ya ba Yusuf wannan sarauta.

Yusuf Muhammadu Buhari shi kadai ne ‘dan shugaban Najeriya, bayan rasuwar ‘dansa na farko Musa.

Jaridar Daily Trust ta ce inda za a samu matsala da wannan nadin sarauta shi ne Mai martaba, Sarkin Daura ya taba ba wani dabam sarautar Talban Daura.

KU KARANTA: Sarkin Daura, Farouk zai ba Shugaba Conde sarauta

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya dira Kano don halartan daurin auren 'dansa Yusuf

A watan Agustan 2019, shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya ziyarci Daura tare da shugaba Muhammadu Buhari, a nan ya yi bikin sallar wannan shekarar.

A wancan lokacin ne Sarki Farouk Umar Farouk ya ba shi sarautar Talban Daura a gaban Duniya.

“Na nada ka Talban-Daura saboda rakiyar da ka yi wa ‘danmu, shugaban kasa Buhari domin ka yi bikin babbar sallah a wannan tsohon gari mai tarihi na Daura.”
“Sarautar Talban-Daura ta mutane masu daraja ce kamar shugaban kasa Conde, mun gode da ziyara.”

KU KARANTA: Kano ta tarbi Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde

Sarkin Daura da Conde
Alpha Conde a Daura Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A wajen wannan bikin da aka yi shekaru biyu da suka wuce, gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya yabi Mai martaba Sarkin Daura a kan wannan karrama wa da ya yi wa Alpha Conde. Har zuwa kafin yanzu Conde, aka sani da wannan sarauta.

Kara karanta wannan

Siyasa a gefe: Hotunan Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari

Abin mamaki sai kuma aka ji Sarki Farouk Umar Farouk ya ba Yusuf Buhari wannan sarauta ba tare da an ji Alpha Conde ya ajiye sarautar, ko an tunbuke shi ba.

A yau ne aka ji cewa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi idin wannan shekara ne a Kaduna, ya yi limancin sallah a filin idi na Murtala Muhammad.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon hadiminsa, Sanata Uba Sani da dinbin Musulmai sun yi sallah a bayan Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Online view pixel