Masarautar Daura za ta bawa Shugaban Guinea sarauta yayin bikin Sallah da Buhari
Shugaban kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde ya iso jihar Katsina a ranar Asabar, 10 ga watan Augusta domin yin bikin sallah tare da takwararsa na Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa Shugaba Buhari, Gwamna Aminu Masari, Mai Martaba Alhaji Farouk Umar Farouk da sauran al'ummar Katsina sun masa tarbar ban girma.
Rahoton ya ce mai magana da yawun shugban kasa Garba Shehu ya ce Shugaba Conde ya zo Najeriya ne don yin bikin babban salla.
Ya yi bayanin cewa Shugaba Conde zai yi sallar Idi tare da Buhari a ranar Lahadi 11 ga watan Augusta kuma daga bisani zai tafi kallon hawan durba a fadar Mai Martaba sarkin Daura, Faruk Umar Faruk.
Sanarwar ta kuma ce za a yi wa Shugaba Conde nadin sarautan gargajiya a masarautar ta Daura.
Shehu ya ce ziyarar ta Conde za ta kara dankon zumuncin da ke tsakanin shugabanin kasashe biyu kuma za su tattauna kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi alakar kasashen su da sauran kasashen duniya.
DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng