Goron Sallah: Muhimman mas’aloli 10 da addinin Musulunci ya kawo a kan biki da sallar idi

Goron Sallah: Muhimman mas’aloli 10 da addinin Musulunci ya kawo a kan biki da sallar idi

Yayin da ake bikin sallar idi a kasashen Duniya, mun kawo maku wasu daga cikon manyan hukunce-hukuncen addinin musulunci a kan wannan ibada.

Legit.ng Hausa ta tsakuro jawaban ne daga wani littafi da babban malamin musulunci, Sheikh Abdul Majeed Ali Hasaan, ya taba rubuta wa a game da sallar.

1. Shin sallar idi wajiba ce?

Ra’ayin Imam Abu Hanifah da Ahmad Ibn Taymiyyah ita ce sallar idi farilla ce. Amma Ahmad Ibn hambal ya tafi a kan cewa idan wasu bangare suka yi, sun sauke nauyin ta ga sauran al’umma. A mazhabar Malikiyyah da Shafi’iyyah, sallar idi sunnah ce mai karfi.

2. Su wanene ya kamata su je sallar idi?

Maza, kananan yara da mata duk za su iya zuwa sallar idi. Haka zalika matafiyi, da kuma mazaunin gida.

3. Mace mai jini za ta iya zuwa idi

Manzon Allah (SAW) ya bada umarni ga mata su tafi wurin sallah ko da kuwa suna yin haila. Illa iyaka, idan sun je musalla, ba za su yi sallah tare da jama’a ba.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Dan Kasar Denmark da ya yi zanen batanci ga Annabi ya koma ga Allah

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya ware, ya yi sallar idi a Bauchi

4. Me ya kamata ayi kafin a tafi wurin sallah?

Malamai sun ce mutum ya yi wanka, ko akalla alwala a gida.

Sannan ya samu asuwaki, ya goge bakinsa.

Imam Ibn Qayyam ya ce ana so mutum ya sa sababbin tufafi masu kyau.

Haka zalika zai yi kyau mutum ya yi koyi da Annabi (SAW), ya sa turare.

5. Za a ci abinci ranar babbar sallah?

Tirmidhi da Ibn Majah sun fitar da hadisin Buraidah (RA) inda ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce ka da a ci abinci a wannan rana har sai an dawo daga wurin sallah.

6. Ya ake yin kabbara

Ana so mutum ya rika yin kabarbari a wannan ranaku a bayyane. Za a rika fadar:

“Allahu Akbar, Allahu Akbar, La Ilaha Illal Lah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lil Lahil hamd!”

Baya ga wannan akwai wasu samfarin kabarbari daga sahabbai irinsu Abdullahi ‘dan Ibn Mas’ud.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Yari ya ce wasu 'Yan siyasan Arewa na kokarin hana shi zama Shugaban APC

7. A ina ake yin sallar idi

A sunnah, ana tsaida sallar idi ne a farfajiya, a samu fili ayi sallah, muddin babu wata larura ba.

KU KARANTA: Buhari yayin sallar idi tare da iyalinsa a fadar Aso Rock

Goron Sallah
Musulmai suna sallar idi
Asali: UGC

8. Yaushe ake kabbara sallar idi?

Za a iya yin sallah duk lokacin da rana ta fito, kafin ta kai tsakiya. Zai fi kyau ayi sallah da wuri, saboda a yanka dabbar layya.

9. Ka’idoji wajen sallar idi

Hadisai a Sahih Bukhari da Sahih Muslim sun nuna ba a yin kiran sallah ko tada ikima wajen sallar idi

Ana yin raka’o’i biyu ne a wannan sallah.

Abdullahi ‘dan Abbas ya ce ba a yin nafila kafin ko bayan sallar idi.

Ana yin kabbara sau bakwai a raka’ar farko, sais au biyar a ta biyu. Ba wajibi ba ne a daga hannuwa yayin kabbara.

Sauraron hudubar idi sunnah ce inji malamai.

10. Bayan an yi sallah

Kara karanta wannan

Abduljabbar: Wasu fitattun Malaman addini da suka shiga hannun Jami'an tsaro a gida da waje

Sahabi Jabir (RA) ya ce Annabi (SAW) ya na canza hanyar da ya biyo bayan sallah, idan zai koma gida.

Ana gaida juna da cewa: ‘Taqabbalal Lahu minna wa minkum’ ko ‘Eid Mubarak’

Jama’an musulmai, Eid Mubarak!

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng