Amaryar tsohon Sarkin Kano Sanusi II ta kammala Digiri na 2 a babbar Jami’ar Duniya

Amaryar tsohon Sarkin Kano Sanusi II ta kammala Digiri na 2 a babbar Jami’ar Duniya

A karshen makon da ya gabata ne aka samu labarin cewa Sa’adatu Barkindo Sanusi ta kammala karatu a jami’ar Buckingham da ke kasar Birtaniya.

Ga wadanda ba su da labari, Hajiya Sa’adatu Barkindo Sanusi, ita ce matar tsohon Sarkin Kano da aka tunbuke, Malam Muhammadu Sanusi II ta hudu.

An yi auren gimbiya Sa’adatu Barkindo Sanusi ne a shekarar 2015, amma sai bayan shekaru hudu ta tare a gidan mai martaba, tsohon Sarkin na Kano.

Gimbiya Sa’adatu Barkindo Sanusi ta fito ne daga gidan Mai martaba Lamidon kasar Adamawa.

KU KARANTA: Tsohin Sarki Muhammadu Sanusi II, zai koma makaranta

Amaryar tsohon Sarkin Kano Sanusi II ta kammala Digiri na 2 a babbar Jami’ar Duniya
Malam Muhammadu Sanusi II da Gogo Sasa Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Kamar yadda aka bayyana a wani shafin Twitter na Masoyan tsohon Sarkin mai suna MS II Dynasty, Gimbiyar ta yi karatu ne a jami’ar Ingilar.

MS II Dynasty ya bayyana haka a ranar Asabar, 20 ga watan Maris, 2021, aka ce Sa’adatu Barkindo ta samu digiri a fannin ilmin tattalin arziki.

Wannan ne karo na biyu da Gimbiya Goggo SaSa ta samu shaidar digiri. A baya ta yi karatun digiri a bangaren ilmin kimiyyar komfuta a nan Ingilar.

Daga baya, Goggo SaSa kamar yadda ake kiran ta a fadar Sarki, ta saki layi, ta bi tafarkin mai gidanta, wanda ya karanci tattalin arziki a ABU Zaria.

KU KARANTA: Tsohon sarkin Kano, ya zama khalifan Tijjaniyya a Najeriya

Amaryar tsohon Sarkin Kano Sanusi II ta kammala Digiri na 2 a babbar Jami’ar Duniya
Malam Muhammadu Sanusi II da Gogo Sasa Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Ga abin da mutane ke cewa a dandalin Twitter:

“Ina taya ta murna, da fatan samun nasar a gaba.” Inji Teemah.

Wani ya ce: “Ilmin tattalin arziki ko? Amma da a Jami’ar Bayero ta yi karatun, da ya fi”

Mujiburrahman Saminu ya ce: “Masha Allah. Allah ya yi mata jagora, ya kuma sa wa ilmin albarka.”

“Ilmin tattali a Birtaniya. Ba zan ce komai ba tukuna.” Inji Ghali Yusuf.

“Masha Allah, Ina taya ki murna Gogo.” - Amb. Yusuf Shamsudeen OFR

Wani mai suna Farfesa Abdussalam, cewa ya yi: “Ina yi maku barka sau dubu-dubu.”

Malam Muhammad Babakura shi ma ya taya tsohuwar gimbiyar murna.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng