Hotunan shugaba Buhari yayin sallar idi, cikin 'yan majalisa da iyalansa a Aso Rock

Hotunan shugaba Buhari yayin sallar idi, cikin 'yan majalisa da iyalansa a Aso Rock

- Shugaba Buhari yayi karamar sallah a fadarsa dake Aso Rock a Abuja, a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021

- Kamar yadda hotunan sallar idin suka nuna, ya sallaci idin tare da iyalinsa da wasu 'yan majalisa

- Bayan kammala sallar, an ga shugaban kasan yana gaisawa da 'yan majalisar tarayyan inda daga bisani ya shiga cikin iyalinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi karamar sallah a fadarsa dake Aso Rock Abuja a yau Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021.

Kamar yadda hotunan da hadiminsa, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Twitter suka nuna, shugaban kasan ya sallaci idin karamar sallah tare da iyalansa, sanatoci da wasu 'yan majalisa.

Bayan kammala sallar idin, sun yi gaishe-gaishe da 'yan majalisar tarayyan tare da daukan hotuna. Daga bisani ya shiga cikin iyalansa inda suka dauka hotuna.

Hotunan shugaba Buhari yayin sallar idi, cikin 'yan majalisa da iyalansa a Aso Rock
Hotunan shugaba Buhari yayin sallar idi, cikin 'yan majalisa da iyalansa a Aso Rock. Hoto daga @Buharisallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo a bude, sun bukaci Buhari yayi wa kasa jawabi

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga 4, sun kwato shanu 170 a Katsina

A wani labari na daban, hukumar majalisar tarayyar kasar nan ta ja kunnen 'yan majalisa, ma'aikata, hadimansu da sauran masu ruwa da tsaki da su ankare da kalubalen tsaron da ake fuskanta, The Punch ta ruwaito.

Majalisar ta ce ta kawo matakan da zasu tabbatar da tsaro tare da gane mutum kafin a basu damar shiga farfajiyar majalisar. An gano cewa majalisar tarayyan na daya daga cikin wuraren da 'yan ta'addan Boko Haram ke kallon kai hari.

An ga wata takarda a ranar Talata da ta gabata wacce aka mika ta ga dukkan Sanatoci, 'yan majalisar wakilai, mataimakin magatakardan majalisar, magatakarda da sauran jiga-jigan majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel