Muhimman abubuwa 8 da ya dace a sani game da marigayi Manjo Janar Ahmed

Muhimman abubuwa 8 da ya dace a sani game da marigayi Manjo Janar Ahmed

  • An kashe Hassan Ahmed, manjo janar na rundar sojin Najeriya a Abuja da daren Alhamis da ta gabata
  • An birne shi ne a ranar Juma’a a Abuja kamar yadda dokokin addinin musulunci ya tanadar da ta sojin kasar nan
  • Janar Hassan ya samu lambobin yabo iri-iri daga wurare daban-daban sakamakon kwazonsa da jajircewarsa

1. An haifi manjo janar Ahmed a ranar 16 ga watan Fabrairun 1968 a garin Maiduguri dama kuma dan asalin Maiduguri ne a jihar Borno.

2. Ya yi karatunsa na sakandare a Comprehensive Secondary School dake Makurdi kafin ya samu gurbin karatu a makarantar sojoji ta NDA a 1988.

KU KARANTA: Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari

Muhimman abubuwa 8 da ya dace a sani game da marigayi Manjo Janar Ahmed
Muhimman abubuwa 8 da ya dace a sani game da marigayi Manjo Janar Ahmed. Hoto daga Nigerian Army HQ
Asali: Facebook

3. Ya kammala karatun horar da hafsin sojoji a ranar 25 ga watan Satumban 1993 inda ya fito a matsayin second Lieutenant.

4. Ya kai matsayin da aka nada shi manjo janar ne kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hoton Yadda Aka Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe

5. Marigayin ya yi digirinsa na fari ne a harkar siyasa sannan yayi na biyu a fannin sanin dabaru a NDA.

6. Ya taba rike mukamin Provost Marshal na sojin kasa kafin mutuwarsa kuma ya rike darektan tsofaffin soji a hedkwatar sojin kasa dake Abuja.

7. Ya yi karatu a fannoni daban-daban a makarantar sojoji dake Jaji da sauran makarantun horar da sojoji dake kasar nan.

8. Sakamakon kwazonsa da dagewarsa wurin yin aiki tukuru a fadin kasar nan, marigayi manjo janar Hassan Ahmed ya samu jinjinawa daga wurare daban-daban wadanda suka hada da Force Service Star, Meritorious Service Star, Distinguished Service Star, Field Command Medal da sauransu.

KU KARANTA: 'Yan uwa 3 sun sheka barzahu bayan sun kwashi garar Amala a Ilorin

A wani labari na daban, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rangwantawa talakawa. Basaraken yayi wannan kiran bayan karbar bakuncin shugaban kasan a fadarsa a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

Ya yi kira ga shugaban kasan da ya inganta tsaro tare da shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

"Muna godiya ga shugaban kasa kan wannan ziyarar kuma hakan zai kara dankon alakarsa da gidan sarauta. Gidansa ne dama can. Ba za mu iya fadin sau nawa ya zo gidan ba ballantana a zamanin marigayin Sarki, a yayin shagali da babu," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng