Mourinho ya dawo da shiri, ya ci kwallo 10 a wasan fari da ya horas da Kungiyar AS Roma
- AS Roma ta yi wasan ta na farko da Kungiyar Montecatini a ranar Alhamis
- Kungiyar ta na sharan fage domin shirya wa wasannin shekarar 2021/2022
- ‘Yan wasan Jose Mourinho suka yi galaba, sun zura kwallaye 10 da nema
Sabon kocin kungiyar AS Roma, Jose Mourinho ya jagoranci ‘yan wasansa sun zuba kwallaye har goma a raga a wasan farko da suka buga a jiya.
A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, 2021, AS Roma ta kara da kungiyar Montecatini ta Italiya, inda ‘yan wasan Jose Mourinho su ka samu nasara.
Sky Sports ta ce wannan gagarumar nasara da tsohon kocin Real Madrid, Chelsea da Manchester United ya samu a garin Trigoria shi ne na farko.
KU KARANTA: AS Roma ta naɗa Mourinho a matsayin sabon Koci
Montecatini ta na cikin kananan kulob da ake da su a kasar Italiya. Kungiyar ta na buga wa a rukunin Seria D.
‘Yan wasan da suka yi wa Montecatini rubuti
Borja Mayoral ya ci kwallaye uku shi kadai, sannan Carles Perez, Gianluca Mancini, Riccardo Calafiori, Nicola Zalewski sun leka ragar Montecatini.
Nicolo Zaniolo da Amadou Diawara sun ci kwallo guda, sai wani ‘dan wasan Montecatini ya ci ragarsa.
Da aka tashi wannan wasa na kawance da ake buga wa kafin soma wasannin kaka mai zuwa, Montecatini ta ce ba za ta manta da wannan rana ba.
KU KARANTA: Kungiyar Real Madrid ta zabi Kocin da zai maye gurbin Zidane
Jaridar Mirror ta ce tsohon kocin na kungiyar Tottenham ya nuna har yanzu da sauransa. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan rasa aikinsa a kasar Ingila.
Rahoton ya ce AS Roma ta iya yi wa Montecatini wannan dure ne duk da cewa wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar ba su dawo aiki ba tukuna.
‘Dan wasa Bryan Cristante da sabon shigowa Rui Patricio ba su buga wasan ba, ba su dawo daga Euro ba.
Dazu kun samu labari bayan ‘yan kwanaki ya na tangariri babu kulob, Lionel Messi zai sabunta kwantiraginsa da Barcelona, zai cigaba da wasa har 2027.
Lionel Messi ya yarda ya rage kudin da yake karba domin cigaba da zama a kungiyar Barcelona.
Asali: Legit.ng