Kungiyar Real Madrid ta zabi Kocin da zai maye gurbin da Zinedine Zidane ya bari

Kungiyar Real Madrid ta zabi Kocin da zai maye gurbin da Zinedine Zidane ya bari

- Carlo Ancelotti ne ke kan gaba wajen karbar aikin horas da Real Madrid

- Kocin kungiyar Everton ya na shirin komawa kungiyar da ya bari a 2015

- Real Madrid ta daina zawarcin Antonio Conte, ta natsu da tsohon Kocinta

Rahotanni daga jaridar Marca sun tabbatar da cewa kungiyar kwallon kafan Real Madrid za ta sake dauko hayar Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocinta.

Da alamu Carlo Ancelotti wanda ya horas da ‘yan wasan Real Madrid tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015, zai koma kan kujerar da aka kore shi daga kanta.

Carlo Ancelotti mai shekara 61 ne ya jagoranci kungiyar zuwa ga nasarar da ta samu a karo na goma a gasar kofin Turai a hannun Atletico Madrid a Lisbon.

KU KARANTA: Koci 3 da za su iya karbar aikin horas da Real Madrid a 2021/22

Kwanaki kadan da Zinedine Zidane ya bada sanarwar tashinsa daga kungiyar, rade-radi ya soma karfi cewa kocin Everton, Carlo Ancelotti, zai dawo Sifen.

Carlo Ancelotti ya zama kan gaba cikin wadanda ake ganin za su karbi aikin horas da manyan ‘yan wasan kungiyar bayan an yi tunanin kawo Antonio Conte.

Shekaru shida kenan da Ancelotti ya bar Real Madrid, amma har yanzu ‘yan kulob din suna sonsa. Bayan tashinsa ya rike Bayern Munich, Napoli da Everton.

A wani kaulin, manyan ‘yan wasan Real Madrid irinsu Sergio Ramos sun nuna ba su sha’awar Conte.

KU KARANTA: Zidane ya samu sabani da Marcelo, sun yi fada

Kungiyar Real Madrid ta zabi Kocin da zai maye gurbin da Zinedine Zidane ya bari
Carlo Ancelotti Hoto: Sam Bagnall Daga: Getty Images
Asali: Getty Images

Haka zalika kungiyar PSG ba ta da niyyar barin kocinta Mauricio Pochettino ya tashi bayan ‘yan watanni, shi kuma Raul bai shirya karbar irin wannan aiki ba.

Jaridar Cadena SER's 'El Larguero' da Fabrizio Romano sun ce kungiyar Real Madrid na kokarin dauko Ancelotti daga Everton, an daina neman Antonio Conte.

Har ila yau, SB Nation ta ce ana daf da bada sanarwar Ancelotti a matsayin sabon kocin Real Madrid.

Ku na da labari cewa Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid ce ta samu nasarar lashe gasar La-liga na shekarar bana 2020/2021, Real ta kare a matsayin na biyu.

Ƙungiyar ta samu nasara ne bayan ta doke takwararta Real Valladolid a wasan ƙarshe da ci 2-1. Wannan ne karon farko da Atletico ta ci La-liga a shekara bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel