Da Dumi-Dumi: Tsageru Sun Kai Hari Banki, Sun Sheke Dan Jarida da Wasu Mutum 2

Da Dumi-Dumi: Tsageru Sun Kai Hari Banki, Sun Sheke Dan Jarida da Wasu Mutum 2

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar ya nuna cewa wasu ‘yan fashi da makami sun afkawa wani banki a Ilara Mokin, karamar hukumar Ifedore ta jihar Ondo inda suka kashe wani dan jarida da dan sanda yayin lamarin.

Dan jaridar, Olubunmi Afuye, ba da dadewa ba aka dauke shi aiki a matsayin kakakin jami’ar Elizade.

Taswirar jihar Ondo | Hoto: thenationonlineng.net
Da Dumi-Dumi: Tsageru Sun Kai Hari Banki, Sun Sheke Dan Jarida da Wasu Mutum 2
Asali: UGC

Yana kan hanyarsa ta zuwa aiki ne sai kwatsam ya ci karo da lokacin da 'yan fashin ke barna kuma suka harbe shi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce nan ba da jimawa ba zai fitar da karin bayani kan lamarin.

Ku dakace mu don karin bayani...

Asali: Legit.ng

Online view pixel