Da duminsa: Ranar Alhamis Buhari zai kaddamar da fara ginin layin dogon Kano-Kaduna
- Bayan kammala na Legas-Ibadan, za'a fara layin dogon Kano-Kaduna
- Shugaba Buhari da kansa zai kaddamar da fara ginin
- Za'ayi bukin kaddamarwan a jihar Kano
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai kaddamar da fara ginin layin dogon jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna.
Sakataren din-din-din na ma'aikatar sufuri, Dr Magdalene Ajani, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abuja ranar Talata.
Za'a gudanar da bikin kaddamarwan a Zawaciki, karamar hukumar Dawaki ta jihar Kano.
DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo
KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
Za ku tuna cewa yayinda aka kammala ginin layin dogon Legas zuwa Ibadan kuma aka kaddamar da shi, gwamnatin tarayya tace tana shirin fara ginin Kaduna zuwa Kano.
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana hakan.
Amaechi ya yi wannan jawabi ne yayinda ya kai ziyarar wajen gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Amaechi ya bayyana cewa jihar Kano na da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya saboda shahararta da harkar kasuwanci.
A cewar Amaechi, nan zuwa watan Yuli za'a fara aikin hada Kaduna da Kano da kuma Ibadan da Abuja.
Asali: Legit.ng