Mutunci ya fi kudi: Cewar matashin da ya mayar da N2.5m da aka tura masa cikin kure

Mutunci ya fi kudi: Cewar matashin da ya mayar da N2.5m da aka tura masa cikin kure

  • Wani dan Najeriya, Julius Eze, ya mayar da kudi N2.5m da aka tura masa asusun bankinsa
  • Julius bai bata lokaci ba wajen mayar da kudin asusun mutumin da yayi kuskuren
  • Yan Najeriya sun ce mutum irinsa ake bukata a wannan kasar

Wani matashi dan Najeriya, Julius Eze, ya baiwa mutane mamaki bisa wani abin ban sha'awa da yayi.

Tsakanin ranar Juma'a, 9 ga Yuli da Asabar 10 ga Yuli, bayan an kulle bankuna, ya ga an tura masa kudi N2.5m cikin asusunsa.

Ba tare da bata lokaci ba ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa ranar Litinin, 12 ga Yuli zai mayar da kudin banki.

Yace:

"Ina banki yanzu! Ba kudi na bane. da yammacin Juma'a da safiyar Asabar na ga an turo min kudi N2.5m asusuna, daga baya na gano wanda ya turo."
Na tuntubesa domin ya turo akawunt lambarsa don in mayar da kudin yau, bayan tambayoyi da bincike da na gudanar masa sun tabbatar lallai nasa ne.

Kara karanta wannan

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahara Buhari

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Matashin da ya mayar da N2.5m da aka tura masa cikin kure
Mutunci ya fi kudi: Cewar matashin da ya mayar da N2.5m da aka tura masa cikin kure Hoto: Julius Eze
Asali: Facebook

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Eze ya bayyana hujjar cewa ya mayar

Ya ce ya tuntubi mutumin domin tabbatar da cewa lallai kudinsa ne.

Yan Najeriya sun yabawa wannan matashi bisa abinda yayi.

Mutane sun tofa albarkatun bakinsu

Shawil Gambo yace:

Mayarwar itace mafita idan yaki mayaswa ma kamashi za'ayi, amma yakamata suyi masa tukuici saboda wannan gagarumar sadaukarwa da yayi gaskiya Nigeria ta fara gyarua Allah ya hada kanmu mu Musulmai da Christian baki daya ya wadatamu ya kuma azurtamu da halal dinmu.

Asiya Khalid tace:

In Allah yaso sai yashiryeka sakamakon zuchiyarka me tausayi,
Allah katsarkake Mana zukatanmu, muzama masu banbance halak da Haram. Matuqar dan Allah yayi Allah yabashi nashi arziqin yakuma shiryashi yagane gaskiya. Domin inma yachi Haram yachi. Alharamu latadummu wa inda mallatanfa uh, Haram bata qarko ko tayi bata amfanarwa,

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya

Abinda zakachi Haram inkayi haquri zaizomaka a halal kachi chikinnatsuwa, inamasu zaginshi zakumaimaita agaban Allah, matukar baku tubaba.

Haddabi Sabo Ibi yace:

Ai dole ne ya mayar, idan bai mayar ba banki zasu kwashe idan mai shi yayi report. Idan kuma ya cire kudin kafin a fahimci anyi kuskure, za'a zo da EFFC har gida a kamasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng