Rufin Majalisar Tarayyar Nigeria Ya Sake Yoyo Karo Na Biyu Cikin Makonni 3

Rufin Majalisar Tarayyar Nigeria Ya Sake Yoyo Karo Na Biyu Cikin Makonni 3

  • Ruwan sama ya sake yoyo a harabar majalisar tarayyar Nigeria da ke Abuja
  • Wannan shine karo na biyu da rufin majalisar ke yoyon ruwa cikin makonni 3
  • Shugaban majalisar Ahmad Lawan ya ce wannan alama da ke nuna majalisar na bukatar gyara

A karo na biyu cikin makonni uku, rufin babban ginin majalisar tarayyar Nigeria a Abuja ya sake yoyo bayan ruwan sama kaman da bakin kwarya da aka yi a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Ruwan ya zuba ne a hanyar da ake bi domin shiga zauren majalisun wakilai na tarayya da sanatoci kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Rufin Majalisar Nigeria Ya Sake Yoyo Karo Na Biyu Cikin Makonni 3
Rufin Majalisar Tarayyar Nigeria Ya Sake Yoyo Karo Na Biyu Cikin Makonni 3. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

A ranar 22 ga watan Yuni, rufin majalisar ya yi yoyon ruwa bayan ruwan sama da aka yi, nan take ma'aikatan majalisar suka shiga aikin kwashe ruwan da goge-goge.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru

Sai dai a wannan karon yan majalisar ba su cikin zauren majalisar a lokacin da rufin ya sake yoyo domin ba su zama a ranar Litinin.

Bayan ruwan saman, an gano ma'aikata da tsumma suna ta kwalfe ruwan da ya zuba cikin harabar majalisar.

Abin da Shugaban Majalisar Ahmed Lawan ya ce game da yoyon ruwan

Bayan yoyon ruwan na farko, Shugaban majalisar Ahmad Lawan ya ce zubar ruwan alama ne da ke nuna tabbas ginin majalisar na bukatar gyara.

Shugaban majalisar ya ce tuni ya kamata a yi wa ginin majalisar garambawul yana mai cewa tunda aka gina shi shekaru da dama ba a taba yin wani babban gyara ba.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Lawan ya ce:

"Yoyon ruwan alama ce da ke nuna wa karara cewa matakin da matakin da suka dauka tun farko shine abin da ya dace.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

"Kowa ya san cewa wannan wurin na bukatar gyara."

A shekarar 2019, majalisar ta ware Naira biliyan 30 domin yin gyare-gyare a harabar majalisar.

Sai dai hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin yan Nigeria da ke ganin kudin da aka ware ya yi yawa domin gyaran.

Sai dai babu wani gyaran da aka yi tunda aka ware Naira biliyan 9 domin gyaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164