Euro 2020: Italiya ta doke kasar Ingila, ta zama gwarzon kasashen nahiyar Turai
- Italiya ta yi galaba a kan kasar Ingila a wasan karshe na gasar Euro 2020
- Kasar Italiya ce gwarzon wannan karo bayan doke Ingila a bugun finariti
- Marcus Rashford, Jadon Sancho, da Bukayo Saka ne su ka barar wa Ingila
A ranar Lahadi, 11 ga watan Yuli, 2021, kasar Italiya ta yi nasara a wasan karshe na kofin nahiyar Turai.
Italiya ta doke kasar Ingila ne a babban filin wasanta na Wembley a bugun finariti. An kai ga hakan ne bayan an tashi 1-1 a cikin minti 120 da ake yi.
‘Dan wasa Luke Shaw ne ya fara zura wa Ingila kwallo a ragar Italiya jim kadan da take kwallon da Bjourn Kuipers mai shekara 48 ya zama Alkalin wasa.
KU KARANTA: Man United ta saye Sancho ana buga gasar Euro
Bayan shafe sa’a guda ana fafata wa, sai ‘dan wasan bayan Italiya, Leonardo Bonucci mai buga wa kungiyar Juventus, ya zura kwallo a ragar kasar Ingila.
Wasa ya kai ga bugun finariti
A haka aka tashi lokacin farko, sai aka kara mintuna 30. A nan ma ba a iya raba kasashen biyu ba, don haka aka tafi ga bugun daga kai - sai mai tsaron gida.
Domenico Beradi, Federico Bernardeschi da Leonardo Bonucci su ka ci wa Italiya bugun finaritinsu, Jorginho da Andrea Belloti su ka barar da damarsu.
KU KARANTA: Ronaldo ya jawo abin surutu a Euro 2020
Taurari Marcus Rashford da Jadon Sancho sun gagara ci
A bangaren kasar Ingila kuwa, Marcus Rashford da Jadon Sancho da aka shigo da su wasan domin su ci finaritin, duk sun barar, haka zalika Bukayo Saka.
Mai rike da kambun kasar Ingila, Harry Kane da takwaransa, Harry Maguire kadai su ka ci finaritin.
Mai tsaron ragar Italiya, Gianluigi Donnarumma ya iya kabe kwallaye biyu. A karshe kuma ya zama babban gwarzon ‘dan wasan wannan gasa da aka buga.
Wannan rashi a gida ya na nufin Kasar Ingila za ta cigaba da dakon neman kofi a Duniya yayin da yanzu ta shafe shekara 55 rabon ta da yin wata babban nasara.
Asali: Legit.ng