Euro 2020: Ronaldo ya dauke lemun Coca Cola daga gabansa, ya ce shan ruwa ya fi lafiya

Euro 2020: Ronaldo ya dauke lemun Coca Cola daga gabansa, ya ce shan ruwa ya fi lafiya

  • Cristiano Ronaldo ya yi sanadiyyar da kamfanin Coca Cola ta tafka asara
  • Jagoran ‘yan wasan Portugal ya ture lemun Coca Cola da aka ajiye masa
  • Wannan ya sa hannun jarin kamfanin ya ragu da 1.6% a cikin ‘yan sa’o’i

Marca ta ce darajar kamfanin Coca Cola ya sauko da kimanin fam Dala biliyan 4.2 bayan da Cristiano Ronaldo, ya dauke wasu lemu da aka ajiye masa

Yayin da aka shirya ‘yan kwallon Portugal da kocinsu za su zanta da manema labarai a makon nan, sai aka ajiye masu robobin lemun Coca Cola a gabansu.

Cristiano Ronaldo wanda shi ne ke rike da kambun ‘yan wasan kasar Portugal, ya na zuwa wajen hirar, sai ya dauke wasu lemun Coca Cola da su ke gabansa.

KU KARANTA: Zidane ya bar Real Madrid, Ancelotti ya sake dawowa a matsayin Koci

Bayan haka sai ‘dan wasan ya dauko gorar ruwa, ya daga sama, ya yi wa mutanen da suke dakin taron nunin cewa shan ruwa ya fi lafiya ga jikin ‘Dan Adam.

Al’ada ce dai yayin da ake buga gasar Euro na cin kofin Turai a garin Budapest, kasar Hungary, a kan ba ‘yan wasa gorar ruwa da kuma Coca Cola maras sukari.

Asarar Naira Tiriliyan 1 a kudin Najeriya

The Guardian ta ce wannan abin da Tauraron ya yi a ranar Litinin, ya jawo wa kamfanin bakin jini a Duniya.

Hannun jarin Coca Cola ya zazzago daga $56.10 zuwa $55.22 daga yammacin ranar Litinin. Hakan ya na nufin arzikin kamfanin ya sauka zuwa $238bn daga $242bn.

Ronaldo da Coke
Ronaldo ya ce ruwa ya isa Hoto: www.marca.com/en/football
Asali: UGC

KU KARANTA: Ahmed Musa ya bada gudumawar kudi a gina masallaci

Tarbiyyar ‘Dan wasan Duniya, Cristiano Ronaldo

Ronaldo mai shekara 36 a Duniya ya na cikin ‘yan wasan kwallon kafa masu lafiya sosai a Duniya, domin ba ya wasa da atisaye da kuma abin da yake ci da sha.

‘Dan wasan na Juventus ya yi suna wajen bijire wa lemun kwalba irinsu Coca Cola. Hakan ya sa har ya kan gargadi ‘dansa a kan shan lemu da cin kayan kwalama.

“Wasu lokutan ‘da na ya kan sha Coca Cola ko Fanta, sai kuma ya ci soyayyen dankali, ya san ba na son wannan.” Ronaldo yake magana a kan ‘dansa Cristiano Jr.

A kwanakin baya kun ji cewa tsohon shugaban ‘yan wasan kungiyar kwallon kafan Najeriya na Super Eagles, Mikel Obi, ya hadu da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Mai girma gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya tabbatar da wannan a shafinsa na Facebook. Mikel Obi ya nuna yana goyon bayan duk wata takara da gwamnan zai shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng