Jerin tituna 5 da gwamnati ta baiwa Dangote kwangilan N309bn maimakon biyan kudin haraji

Jerin tituna 5 da gwamnati ta baiwa Dangote kwangilan N309bn maimakon biyan kudin haraji

Majalisar zartaswa FEC ta amince da baiwa kamfanin Dangote kwangilan gina titunan kankare guda biyar masu tsawon kilomita 274.9 a kudi N309,917,717,251.35 maimakon kudin harajin da zai biya gwamnati.

TheCable ta ruwaito cewaa Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola, ya bayyana hakan ranar Juma'a, 14 ga Yuli, yayin hira da manema labarai bayan taron majalisar FEC da shugaba Buhari ya jagoranta.

Ga jerin jihohin da Dangote zai yi wadannan tituna:

1. Jihar Borno

a) Bama zuwa Banki (49.153 kilomita) - N51.016 billion

b) Dikwa zuwa Gamboru-Ngala (49.577 kilomita) - N55.504 billion

2. Jihar Kaduna

a) Babban titin Nnamdi Azikiwe, Daga Command Junction zuwa Kawo ((21.477 kilomita) - N37.560 billion

3. Jihar Lagos

a) Epe zuwa Shagamu, titin zai hada jihar Lagos Ogun (54.24 kilomita) - N85.838 billion

4. Jihar Ogun

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta ba Dangote kwangilar yin hanyoyi a maimakon ya biya haraji

a) Obele/Ilaro/Papalanto zuwa Shagamu (100 Kilomita) - N79.996 billion

KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD

Jerin tituna 5 da gwamnati ta baiwa Dangote kwangilan N309bn maimakon biyan kudin haraji
Jerin tituna 5 da gwamnati ta baiwa Dangote kwangilan N309bn maimakon biyan kudin haraji Hoto: TItuna
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Shirin yin aiki maimakon biyan haraji

A cewar Fashola, za'ayi wadannan tituna ne karkashin tsarin bashin haraji don ayyuka.

Hakan na nufin cewa za'a biya Dangote kudin ginin ta hanyar cirewa daga kudin harajin da ya kamata ya biya gwamnatin tarayya.

Fashola ya yi bayanin cewa tun kafin zuwan shugaba Buhari aka samar da wannan tsari amma ba'a aiwatar ba.

Ya ce gwamnatin Buhari ta fara aiwatarwa kuma an yi amfani da shi wajen gina titin Apapa Wharf, Oworonsoki zuwa Apapa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng