Da dumi: Fursunoni 4 sun gudu daga gidan yarin Najeriya dake garin Jos

Da dumi: Fursunoni 4 sun gudu daga gidan yarin Najeriya dake garin Jos

  • Akalla fursunoni hudu sun arce daga gidan gyaran hali dake garin Jos, birnin jihar Plateau
  • Geoffrey Longdien, kakakin gidan yarin ya tabbatar da cewa mutum hudun sun gudu ranar Alhamis
  • Mutum hudun da ake zargin makiyaya ne sun gurfana gaban kotu a shekarar 2020 kafin jefasu kurkuku

Wani rahoton Nigerian Tribune ya nuna cewa akalla fursunoni hudu dake gidan yarin Jos, jihar Pleateau sun gudu, an nemesu an rasa.

Wata majiya ta bayyanawa manema labarai cewa wadannan fursunoni da ake zargin makiyaya ne sun gudu daga gidan yarin ne cikin daren Alhamis, 8 ga Yuli.

The Nation ta kara da cewa makiyayan da suka gudu sun gurfana gaban kotun majistare dake karamar hukumar Barkin Ladi a shekarar 2020.

Kakakin gidan gyara halin, Geoffrey Longdien, ta tabbatar da wannan labari.

Ya bada tabbacin cewa an kaddamar da bincike kan lamarin.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

Da dumi: Fursunoni 4 sun gudu daga gidan yarin Najeriya dake garin Jos
Da dumi: Fursunoni 4 sun gudu daga gidan yarin Najeriya dake garin Jos
Asali: Original

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Tsohon shugaban kasar South Afrika ya mika kansa ga hukuma, ya shiga kurkuku

A bangare guda, biyyaya ga umurnin kotu, tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, ya mika kansa ga hukumar yan sanda domin jefashi cikin kurkuku na tsawon watanni 15.

Reuters ta ruwaito cewa Kakakin hukumar yan sanda, Lirandzu Themba, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar 7 ga Yuli, inda yace yanzu haka Zuma na hannunsu.

Kotu ta yanke hukuncin daure tsohon shugaba Zuma kan laifin kin amsa sammacin kotu kan zargin rashawa da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel