Yau Majalisar Ingila za ta binciki yadda Gwamnatin Buhari ta kudunduno Nnamdi Kanu

Yau Majalisar Ingila za ta binciki yadda Gwamnatin Buhari ta kudunduno Nnamdi Kanu

  • Ana sa rai Majalisar Birtaniya ta tabo maganar Shugaban IPOB Nnamdi Kanu
  • Idan an zauna a ranar Laraba, Patrick Lord Alton zai bukaci a binciki lamarin
  • IPOB ta ce an kama Kanu a kasar waje da karfi da yaji, aka kawo shi Najeriya

Jaridar Punch ta rahoto cewa Majalisar Birtaniya ta shirya zama domin tafka muhawara kan yadda aka dawo da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, gida.

‘Yan majalisar na Ingila za su tattauna a game da salon da jami’an tsaro da hukumomi su ka bi, su ka cafke Nnamdi Kanu daga kasar Kenya zuwa kasarsa, Najeriya.

Rahoton da jaridar Sahara Reporters ta fitar a ranar Talata da yamma, ya ce ana sa ran cewa za a yi wannan zama ne a safiyar yau Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021.

KU KARANTA: Sato Kanu aka yi daga kasar waje ta barauniyar hanya - Soyinka

Gwamnatin Birtaniya ta bakin wani jami’in jakadancinta, ta ce an yi ram da Nnamdi Kanu wanda yake da takardar zama ‘dan kasar Ingila ne, a wata kasa dabam.

Bayanin da majalisar Birtaniya ta fitar a shafinta na yanar gizo, ya nuna cewa wannan zargi ya na cikin abubuwan da za ayi muhawara a kai idan an zo zaman yau.

'Dan jam'iyyar adawa, David Patrick Lord Alton, ya na so ayi bincike

‘Dan majalisa, David Patrick Lord Alton mai wakiltar mazabar Liverpool, zai bijiro da wannan magana a majalisa, domin a binciki aikin na gwamnatin Najeriya.

David Patrick Lord Alton mai shekara 70 ya yi suna wajen kare Bil Adama daga cin zarafi a majalisa.

KU KARANTA: Babu yadda za mu yi da kai - Ingila ga Kanu

Majalisar Birtaniya
'Yan Majalisar Birtaniya a wani zama Hoto: www.democraticaudit.com
Asali: UGC
“Lord Alton na Liverpool zai tambayi gwamnatin Ingila kokarin da ta yi wajen binciken rawar da Kenya ta taka na damke, Nnamdi Kanu tare da ci masa zarafi.”

‘Dan majalisar zai nemi jin yadda aka kamo wannan mutum da ya kira ‘dan gwagwarmaya daga kasar waje ba tare da zabinsa ba, da taimakon da Ingila ta ba shi.

A wata kasar Afrika ta gabas aka cafko Kanu - IPOB

Kungiyar IPOB da Mazi Nnamdi Kanu mai shekara 54 yake jagoranta, ta hakikance a kan cewa an kama shi ne a wata kasa da ke yankin gabashin nahiyar Afrika.

Lauyan wannan mutumi da gwamnatin Najeriya ta ke farauta, Ifeanyi Ejiofor, ya yi wannan ikirari.

Amma Jakadan kasar Kenya, Wilfred Machage, da hukumomin kasar sun musanya wannan zargin da ake yi masu, su ka ce ba cikin Kenya aka kamo Kanu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng