Sunday Igboho zai yi shari’a da Gwamnatin Buhari a kan tsare masa yara 13 da DSS ta yi

Sunday Igboho zai yi shari’a da Gwamnatin Buhari a kan tsare masa yara 13 da DSS ta yi

  • Lauyan Sunday Adeyemo ya ce sun shigar da Gwamnatin Tarayya a kotu
  • Ana kalubalantar tsare hadiman Sunday Igboho da jami’an DSS su ka yi
  • Za ayi shari’a tsakanin Gwamnatin Najeriya da Lauyoyin wannan mutumi

Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya dumfari kotun tarayya a Abuja, ya na karar jami’an tsaro da hukumomin gwamnatin tarayya.

Punch ta fitar da rahoto cewa Sunday Igboho ya nemi kotu ta sa a fito masa da wasu hadimansa da jami’an DSS masu fararen kaya su ka cafke kwanan baya.

Sunday Adeyemo ya na zargin cewa an kama wadannan yaran na sa ne a gidansa da ke shiyyar Soka a garin Ibadan, jihar Oyo, a ranar 1 ga watan Yulin nan.

KU KARANTA: Igboho: Gwamnonin kudu maso yamma sun kira taron gaggawa

Lauya ya je kotu a madadin Sunday Igboho

Babban lauyan da yake kare wannan mutumi, Yomi Aliyu (SAN), ya shaida wa jaridar cewa sun shigar da kara a kotu, su na neman a fito da mutanensu har 13.

Sai dai Barista Yomi Aliyu (SAN) bai bada wannan karin bayani a game da wannan shari’a ba.

“Mun shigar da karar ne a yau.”

Da manema labarai suka tuntubi lauyan a game da kokarin da su ke yi, sai ya ce sun kai maganar gaban Alkalin kotun tarayya, suna neman a bada belinsu a kotu.

KU KARANTA: Sunday Igboho ya aikawa Gwamnatin Tarayya sako

Sunday Igboho
Sunday Igboho Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

DSS sun hana Igboho sadu wa da Lauyoyinsa

Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki ya fitar da jawabi a ranar Laraba, inda ya ce jami’an DSS sun hana lauyoyi su hadu da wannan mutum da ke tsare.

Jami’an DSS sun dura gidan Igboho ne a tsakar daren ranar Alhamis da ta wuce, su ka ce sun kama mutane, sannan sun samu makamai a gidan Adeyemo.

Tuni dai wannan mutumi ya karyata maganar, ya ce DSS ne su ka ajiye makaman a cikin gidansa.

Bayan haka kungiyar Ilana Omo Oodua ta bakin kakakinta, ta ce za a saki wasu mutane kusan 50 da aka kama suna zanga-zanga kwanakin baya a garin Legas.

Ku na da labari cewa Lauyan Nnamdi Kanu ya bada tabbacin za a fito da shugaban na kungiyar IPOB kwanan nan, ya ce ba za a iya daure shi a gidan kurkuku ba.

Lauyan ya ce babu wani mahaluki da ya isa ya hana shi tsayawa Nnamdi Kanu a kotu. Sannan yace Kanu ya na samun lafiya bayan muzguna masa da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng