Kashi 70% na Kanawa ka iya fadawa shan kwaya nan zuwa 2050

Kashi 70% na Kanawa ka iya fadawa shan kwaya nan zuwa 2050

  • Ana fargabar kashi 70 na Kanawa za su zama ‘yan kwaya idan ba a dauki mataki ba
  • An yi kiyasin akwai masu shan kwaya fiye da miliyan uku a jihohin Arewa maso Yamma
  • A Jihar Kano kadai akwai mutum miliyan daya masu shan kwaya

An yi hasashen cewa muddin ba a yi wani abin a zo a gani ba wajen shawo kan matsalar kwaya da ake samu a yanzu, kashi 70 cikin 100 na mutanen Jihar Kano ka iya fadawa ko zama masu shan kwaya nan da shekarar 2050.

Manaja Daraktan, Cibiyar Kula da Lafiyar Jama'a da Ba da Shawara ta Almustaqbal, Dokta Idris Salisu Rogo ya bayyana haka a Karamar Hukumar Tsanyawa na Jihar Kano a ranar Alhamis, yayin kaddamar da filin da za a yi amfani da shi wajen gina cibiyar kula da lafiyar masu shan miyagun kwayoyi, rahoton DailyTrust.

Idan an kammala gina cibiyar, za ta zama irinta mafi girma a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita

Yace:

“A yanzu haka, akwai masu ta'ammali da miyagun kwayoyi sama da miliyan uku a jihohin Arewa maso Yamma, cikin wadannan, kimanin miliyan 1.07 suna cikin Jihar Kano ne.
Idan ba mu yi wani kokarin shawo kan wannan matsalar ba a yanzu, kusan kashi 70 na mutanen jihar za su iya shiga cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi,”

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Kashi 70% na Kanawa ka iya fadawa shan kwaya nan zuwa 2050
Kashi 70% na Kanawa ka iya fadawa shan kwaya nan zuwa 2050 Hoto: Kano

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Cibiyar za ta horar da mutane da ilmantar da su

Ya bayyana cewa cibiyar da ake sa ran kammalawa a cikin watanni takwas za ta samu damar karbar kusan masu mu'amala da kwayoyi dubu biyar wadanda za a horar da su a fannoni daban-daban da ilimi domin zama mutane na gari a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Daraktan ya kuma ce:

“Za a yi amfani da wannan filin mai girman kadada biyu wajen ginin. Manufarmu ita ce samar da gyara halayya wanda zai shafi kai da hannu da zuciya kamar yadda Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na Magunguna da Laifuka (UNODC) ya ba da shawara.
“Za mu tabbatar da cewa mutanen da za su zo nan don gyara musu halayya za su bar nan a matsayin mahaddata Alkur’ani Mai Girma.
“Mun riga mun kammala shirye-shirye tare da Jami’ar Karatu daga Gida (NOUN) wajen samar da cibiyar karatu a nan ga wadanda suke son ci gaba da karatu.

Ya kara da cewa duk wani gyaran halayya da zai yi nasara, bai kamata ya mai da hankali kan bada magani ba kawai, don haka suna da niyyar ba da horon sana’o’i da kuma aikin gyaran tunani.

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Hakimin Tsanyawa, Alhaji Mu’awiya Abbas Sanusi ya yaba da yadda aka samar da cibiyar a yankin, lura da cewa matasa a matsayinsu na shugabannin gobe suna bukatar irin wannan gyaran halin.

Kara karanta wannan

Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa filin da za a gina cibiyar wani mai taimakon al’umma a yankin, Alhaji Shehu Ashaka shi ne ya bada filin kyauta.

Ya bayyana cewa domin magance matsalar, dole ne mutane su nemo bakin zaren daga tushe sannan kowa ya fada wa kansa gaskiya.

Ya ce an samar da cibiyar a wajen ne lura da wadanda za su amfana da ita za su fito ne daga dukkan sassan Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel