Tsohon shugaban kasar South Afrika ya mika kansa ga hukuma, ya shiga kurkuku
- An jefa tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, cikin gidan yarin Estcourt
- Yan sanda sun yi masa barzanar damkesa idan har yaki bin umurnin kotu
- Tsohon shugaban kasan ya yi kokarin gujewa shiga kurkukun shekara da rabi da aka yanke masa
Biyyaya ga umurnin kotu, tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, Jacob Zuma, ya mika kansa ga hukumar yan sanda domin jefashi cikin kurkuku na tsawon watanni 15.
Reuters ta ruwaito cewa Kakakin hukumar yan sanda, Lirandzu Themba, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar 7 ga Yuli, inda yace yanzu haka Zuma na hannunsu.
Kotu ta yanke hukuncin daure tsohon shugaba Zuma kan laifin kin amsa sammacin kotu kan zargin rashawa da ake masa.
Wannan shine karo na farko da za'a tsare wani tsohon shugaba a kasar Afrika ta kudu.
Da farko Zuma ya ki mika wuya ga hukumar amma daga baya ya saduda.
Gabanin haka yan sanda sun gargadesa ya mika wuya ko kuma su damkeshi.
DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota
An jefa Zuma gidan yarin Estcourt
CNN ta ruwaito cewa hukumar gidajen gyara halin kasar sun tabbatar da cewa an shigar da Zuma gidan yarin Estcourt dake kusa da gidansa a KwaZulu-Natal.
BBC ta ruwaito diyar tsohon shugaban kasan, Dudu Zuma-Sambudia da cewa mahaifinta na kan hanyar zuwa gidan yari.
Ana tuhumar tsohon shugaban kasan da hannu dumu-dumu cikin rashawa lokacin da yake kan mulki.
Za'a halastawa mace auren maza fiye da guda a Afrika ta kudu
Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Afrika ta kudu ta sanar da cewa tana shirin kafa sabuwar dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya kamar yadda maza ke auren mace fiye da daya.
A cewar rahoton iharare, sabuwar dokar za tayi bayani game salon auratayyan da basu hallata ba.
Rahoton yace takardar da ma'aikatar ta fitar wannan makon ya nuna cewa babu adalci da daidaito kan dokar auren da ake amfani da shi yanzu.
Asali: Legit.ng