Duk jirgin da ya yi jinkirin tashi na awa biyu dole ya mayarwa fasinja kuɗinsu, FG

Duk jirgin da ya yi jinkirin tashi na awa biyu dole ya mayarwa fasinja kuɗinsu, FG

  • Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta bullo da sabbin dokoki na hukunta kamfanoni da ke bata wa fasinja lokaci
  • Ma'aikatar sufurin ta ce duk kamfanin da ya bata wa fasinja lokaci kasa da awa daya zai bawa fasinjoji abin motsa baki sannan ya nemi afuwarsu
  • Idan kuma an bata wa fasinja lokaci daga awa biyu zuwa sama, za a mayar masa kudinsa, a bashi wurin kwana idan cikin dare ne, sannan a biya shi kudin zuwa filin jiragen sama tare da neman afuwa

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce dole kamfanonin sufurin jiragen sama su mayarwa fasinjoji kudin tikitinsu baki daya idan har aka samu jinkiri da ya kai na awa biyu kafin ainihin lokacin tashi, The Cable ta ruwaito.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin jawabi da ya yi wurin taron manema labarai da tawagar shugaban kasa ta kira a Abuja.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

Ya bukaci fasinjoji su rika bin hakokinsu duk lokacin da kamfanonin sufurin jiragen saman suka take musu hakkinsu.

Ya ce:

"A tafiye-tafiye na cikin kasa, jinkiri na kasa da awa daya, kamfani zai bawa fasinja abin motsa baki, kiran waya ko sakon kar ta kwana ko imel. Su aika muku imel ko sakon kar ta kwana ko su kira ku su ce, 'Ina neman afuwarka, zan yi jinkirin awa daya."
"Jinkirin awa biyu ko fiye da hakan, kamfanin sufurin jirgin zai mayarwa fasinja cikkaken kudin tikitin da suka biya.

KU KARANTA: Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

"Jinkiri tsakanin karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba, kamfanin zai samar da wurin kwana a otel, abinci, abin motsa baki, kira na kyauta biyu, sakon kar ta kwana, imel da kudin mota na zuwa da dawowa filin tashin jiragen sama."

Ya ce dukkan wannan dokokin sun shafi tafiya zuwa kasashen waje kamar yadda rahoton na The Cable ya bayyana.

Sirika ya ce ma'aikatarsa ta sufurin jiragen sama ta fara hukunta wasu kamfanonin sufurin da ke take hakkin kwastomominsu.

Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara

A wani labarin daban, wata babban kotun jihar Kano, a ranar Talata ta ci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tarar N800,000 bayan ya janye karar bata suna da ya shigar kan mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian, Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje ya maka mawallafin Ja'afar Ja'afar a kotu be saboda labari da bidiyon da ya wallafa inda aka gano wani da aka shine ke saka kudaden kasashen waje a cikin aljihunsa.

Kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Suleiman Danmallan, wadda ta amince da dakatar da shari'ar, ta umurci gwamnan ya biya Ja'afar Ja'afar da kamfaninsa na jaridar N400,000 kowannensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: