Mun aike 'yan bindiga masu yawa ga Mahaliccinsu, COAS Farouk Yahaya

Mun aike 'yan bindiga masu yawa ga Mahaliccinsu, COAS Farouk Yahaya

  • Shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Farouk Yahaya ya sanar da cewa dakarunsa sun aike da 'yan bindiga da yawa lahira
  • Kamar yadda ya sanar bayan karin girman da Buhari yayi masa, Yahaya yace suna can zasu amsa laifukan da suka yi a wurin Mahaliccinsu
  • Yahaya wanda ya tashi daga Manjo Janar zuwa Laftanal Janar a yau Laraba, shine tsohon kwamandan OpHK

Mun aike 'yan bindiga lahira ga Mahaliccinsu

Shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya a ranar Laraba ya ce dakarunsa sun aike da 'yan bindiga masu yawa lahira inda zasu amsawa Ubangiji laifukan da za a tuhumesu dasu.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, babban kalubalen dake addabar kasar nan a halin yanzu shine ayyukan miyagun 'yan bindiga.

Aso Villa, Abuja

A yayin jawabi ga manema labari na gidan gwamnati bayan kara masa girma zuwa mukamin Laftanal Janar, Yahaya ya ce sojoji suna matukar azabtar da 'yan bindiga yanzu.

KU KARANTA: Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19

Mun aike 'yan bindiga masu yawa ga Mahaliccinsu, COAS Farouk Yahaya
Mun aike 'yan bindiga masu yawa ga Mahaliccinsu, COAS Farouk Yahaya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a

A yayin da aka bukace shi yayi tsokaci kan umarnin da Buhari ya bada game da 'yan bindiga da sauran masu laifuka inda yace a yi musu magana da yaren da suke ganewa, ya ce: "Abinda muka fara yi kenan. Da yawansu an aikesu ga Mahaliccinsu domin su amsa laifukansu, za mu kuma cigaba da yin hakan."

Wadanda suka halarci karin girman

Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban sojin sama, Air Marshal Isiaka Amao, shugaban fannin binciken sirri na tsaro, Manjo Janar Sunday Adebayo, darakta janar na hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Bichi da kuma Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, duk sun halarci wurin karin girman da kawata Yahaya.

Kafin nada shi matsayin shugaban sojin kasa, shine kwamandan rundunar Operation Hadin Kai dake yankin arewa maso gabas, Daily Trust ta ruwaito.

A wani labari na daban, kungiyar malamai ta kasa baki daya (NUT), reshen jihar Kaduna, ta maka Gwamna Nasir El Rufai gaban kotun masana'antu kan zarginsa da take da kutse cikin al'amuranta.

A tare da gwamnan, kungiyar ta hada da antoni janar na jihar, hukumar makarantun firamare da kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Daily Nigerian ta ruwaito.

A lokacin da aka kira shari'ar gaban mai shari'a Ayodele Obaseki-Osaghae, lauyan mai kara, Samuel Atung ya sanar da kotun cewa an mikawa dukkan wadanda ake kara sammaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel