Da duminsa: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya
- Maniyyata sun fara isa Makkah domin gudanar da Ibadar Hajji na bana
- Gwamnatin Saudiyya za ta sanar da ranar da watar Hajji zata kama
- Bana babu wanda zai gudanar da Hajji daga wajen kasar Saudiyya
- Mutum 60,000 kacal aka amincewa yin hajji bana
Za'a fita neman jinjirin watan Zhul-Hijja a kasar Saudiyya ranar Juma'a, 29 ga Dhul Qa'adah 1442 bisa kalandan Ummul Qura, wanda yayi daidai da ranar 9 ga Yuli, 2021, rahoton Haramain Sharifain.
Duba watan Zhul-Hajji ne zai bayyana ranakun Hajji ga Mahajjata da kuma Sallar Layya ga sauran al'ummar Musulmai a fadin duniya.
Za'a yi duban watan na farko ne a jami'ar Al Majmah dake Sudair, yayinda za'a sake dubawa a Tumair da kuma sauran wurare.
Kotun Kolin Saudiyya ce zata sanar da sakamakon gani ko rashin ganin watan da yammacin ranar Juma'a.
DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya
KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari
Yan Najeria babu Hajji bana
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta soke aikin Hajjin mahajjata daga kasashen duniya na shekarar 2021.
Shugaban na NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fatima Usara, jami'ar hulda da jama’a ta hukumar ta fitar ranar Asabar a Abuja.
Mista Hassan ya ce NAHCON na mutunta hukuncin da Saudiyya ta yanke game da wannan batun komai tsananin hukuncin ga hukumar da kuma maniyyata a duk duniya.
Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu
Abdulwasiu A B Labbaika yace"
Ko sun gani dan Allah ba sai sun fada muna ba tinda sunce Aikin Hajjin bana nasu ne su kadai
Abdullahi Al-katsinawy Muhammad Yace:
Hmmm wai wadanda suka Hana aikin hajjin bana saboda wani iya shege (Corona) sune suke fada mana zasu fita neman wata
Nura Sayyadi Yace:
Allah kabamu ikon zuwa kafin ahanamu zuwa gabadaya
Hãmzá Ãhméd Ìñûwá
Ubangiji ALLAH ya tabbatar musu da ganin watan ya kuma basu ikon bayyanawa duniya gaskiyar lamarin.
Asali: Legit.ng