Abin mamaki yayin da wani mutum ya kara aure da kudin tallafin da kungiya ta ba shi domin kula da ’ya’yansa 7
- Wani mutum da wata kungiya mai zaman kanta ta ba shi kudi domin fara kasuwanci kuma ya kula da ’ya’yansa guda 7 ya kashe kudin inda ya yi amarya
- Wani mai amfani da kafar sada zumunta ne ya bada labarin wanda abokinsa yake aiki da kungiyar agajin
- Masu amfani da shafukan sada zumunta na ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin
Wata Kungiya mai zaman kanta (NGO) ta bayar da gudummawar N100,000 ga wani magidancin da ke fama da yadda zai dauki nauyin iyalinsa da zimmar ya kama harkar kasuwanci.
Sai dai abin mamaki a nan, magidancin ya buge da kashe dukkan kudaden wajen kara aure, kamar yadda wata mai amfani da kafar sada zumunta da sunan @purpleandflawed ta wallafa a shafinta na sada zumuntar,
Ta ce mutumin ya yanke shawarar kashe kudin ne wajen shirya bikin auren mata ta biyu, a maimakon yayi amfani da tallafin kan sharadin da aka ba shi.
Kodayake mai ba da labarin ta yi iya kokarinta wajen ganin ba ta ba da cikakken bayani game da magidancin ba da kuma wurin da yake, amma labarin yana samun gindin zama sosai a shafukan sada zumunta.
DUBA NAN: Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed
KU KARANTA: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya
Mutane sun tofa albarkatun bakinsu
Ga dai muhawarar da masu amfani da shafukan sada zumunta ke yi, kamar yadda za ku gani a kasa akwai abubuwa masu kayatarwa da Legit.ng ta tattara kan muhawarar:
Wani mai suna @BBB26712829 ya ce:
Koda a ce matar aka bai wa kudaden, to ai za ta mika masa kudin wanda daga bisani zai almubazzarantar da su. Lura da ire-iren wadannan abubuwan, ban ga dalilin da ya sa har yanzu kungiyoyi masu zaman kansun ke mayar da hankali a tallafin nasu zuwa yankin Arewacin Najeriya ba.
Wani kuma mai amfani da sunan @Tisheyy ya bayyana cewa:
"Wannan fadar da ake yi gaskiya cewar "Idan ka tallafa wa namiji to shi kadai ka tallafa wa; amma idan ka tallafa wa mace to dukkan al’ummarta ka tallafa wa."
A cewar mai suna @godwinfrance ya nunar da cewa:
"Masu kungiyar agajin ya kamata a ce tun da farko sun fahimci cewa bai dace ka hannunta wa wadanda za ka tallafa wa kudi a hannunsu ba. Akwai rahoto na musamman game da hakan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi. Na biyu kuma ya dace kungiyar ta samu rahoton.
Asali: Legit.ng