Da duminsa: Ana musayar ruwan wuta tsakanin 'yan daba da jami'an tsaro a Legas

Da duminsa: Ana musayar ruwan wuta tsakanin 'yan daba da jami'an tsaro a Legas

  • Jami'an tsaro a jihar Legas a halin yanzu suna musayar ruwan wuta da 'yan daba a Apapa
  • Kamar yadda ganau suka tabbatar, jami'an tsaron sun je korar 'yan daban ne amma suka ki tafiya
  • 'Yan daba sun dinga jifan jami'an tsaron yayin da jami'an suka dinga watsa barkonon tsohuwa da harbi

Apapa, Legas

'Yan daba wadanda aka fi sani da Area Boys a jihar Legas suna musayar wuta da jami'an tsaron hadin guiwa a Apapa dake jihar Legas a halin yanzu.

Jami'an tsaron hadin guiwar sun hada da 'yan sanda, jami'an hukumar kula da cunkoson tituna na jihar Legas da sojoji.

Ganau sun ce jami'an tsaron hadin guiwar sun isa get na farko na Tin-Can dake Mile 2 babbar hanyar Apapa domin fatattakar bata-garin da ake zargi da aikata laifuka a yankin.

KU KARANTA: Dama na sha alwashin kai ka kasa, Asari Dokubo yayi martani kan kamen Nnamdi Kanu

Da duminsa: Ana musayar ruwan wuta tsakanin 'yan daba da jami'an tsaro a Legas
Da duminsa: Ana musayar ruwan wuta tsakanin 'yan daba da jami'an tsaro a Legas
Asali: Original

'Yan daba sun fara jifa, jami'ai na watsa barkonon tsohuwa da harbi

An gano cewa 'yan daban sun ki tafiya, lamarin da ya kawo fito-na-fito tsakanin bangarorin biyu.

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan daban sun fara jifan jami'an tsaron da duwatsu da kwalabe.

"Domin korar 'yan daban, jami'an tsaron sun fara watsa barkonon tsohuwa. 'Yan achaba sun bi ayari inda suka shigarwa 'yan daban inda daga nan aka fara jin harbe-harben bindiga," daya daga cikin 'yan achaban ya sanar da Daily Trust.

KU KARANTA: Cikakken sunayen janarori 114 da sauran sojin kasa da aka sauyawa wurin aiki

A wani labari na daban, hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel