Abubakar Malami ya musanta wallafa rubutun batanci a kan Igbo da Hausawa
- AGF Malami ya ce babu kanshin gaskiya a zargin da ake masa na cewa ya yi wani rubutu na cin fuska a kan Igbo da Hausawa
- Mai magana da yawun Malami, Umar Gwandu ya bayyana cewa ministan shari’a bai rubuta ko tunanin irin wannan sakon ba
- Gwandu ya bayyana cewa wasu bata gari ne suka kirkiro rahoton kuma suka yada shi wadanda ke da niyyar lalata martabar Malami
Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Mista Abubakar Malami (SAN), ya karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa ya yi wani rubutu na batanci kan Igbo da Hausawa.
Wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Umar Gwandu ya fitar, ta ce Malami bai rubuta ko tunanin irin wannan sakon ba, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Hotuna da bidiyon tsalelliyar Shuwa Arab da mataimakin gwamnan Neja yayi wuff da ita
“Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a bai rubuta ba kuma bai taba tunanin yin rubutu ko sanya irin wadannan kalaman na batanci a kan wata kabila ko bangare na al’adu daban-daban a kasar ba.
"An san Malami dan kishin kasa ne kuma mara nuna bangaranci wanda ya yi imani da daidaito, gaskiya da adalci ga kowa ba tare da la’akari da son zuciya ga kabila, wuri ko jinsi ba,” inji shi.
A cewar Gwandu, illar da ke tattare da kalaman, rashin wayewar kai da nuna bangaranci gami da rashin girmama bambancin dan Adam ya sa ba za a iya yarda da cewa wallafar ya fito ne daga Malami ba.
KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa a 2023: Tana shirin karewa Atiku, Kwankwaso, Tambuwal da sauransu
“Ofishin Atoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a na kira ga jama’a da su yi watsi da wallafar. Makirai ne suka kirkire shi sannan kuma suka yada shi da nufin lalata martabar Ministan," in ji Gwandu.
A wani labarin na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji, 'yan sanda da sauran hukumOmin tsaro da su tabbatar da gaggauta ceto dukkan wadanda aka sace.
Buhari ya bada wannan umarnin ne a ranar Litinin ta wata takarda da Garba Shehu ya fitar a Facebook inda ya nuna damuwarsa kan harin jihohin Kaduna da na Neja wanda yace duk dalibai aka kwashe.
A yayin tabbatar da ci gaba da tura karin jami'ai dukkan yankunan da ke da matsala, shugaban kasan yayi kira ga hukumomin tsaron da su yi aikin gaggawa wurin ceto dukkan 'yan makarantan a jihohin tare da dawo dasu gida lafiya.
Asali: Legit.ng