Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a Zangon kataf ta Kaduna
- 'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun shiga yankin Katsit dake karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna
- Duk da har yanzu ba a san yawan barnar da suka yi ba, an gano cewa sun kutsa wata kasuwar aladu ta yankin
- Kamar yadda wani wanda ya tsallake rijiya da baya ya sanar, jama'a suna ta tserewa sansanin sojoji domin samun mafaka
Zangon Kataf, Kaduna
Miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kutsa yankin Katsit na karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.
A kalla mutum uku ne suka samu miyagun raunika yayin harin da ya faru a daren Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta tattaro cewa, bayan 'yan bindigan sun shiga yankin, sun fara harbe-harbe babu kakkautawa.
KU KARANTA: Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari
Ganau ya bada labari
Wani dan achaba wanda ya sha da kyar yayin harin ya sanar da cewa ya ga 'yan biindigan na tahowa daga wani gidan biredi inda suka karasa shiga wata fitacciyar kasuwar aladu.
"Da gaggawa na juya kan babur dina tare da fasinjana zuwa wani sansanin sojoji na rundunar Operation Safe Haven inda na ga jama'ar da suka tsira daga 'yan bindigan.
“Masu wucewa da tarin yawa tare da ababen hawa dankare da fasinjoji duk suna wurin yanzu haka," yace.
KU KARANTA: Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda
Yankin Katsit a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna wuri ne dake da iyaka da garin Kafanchan, babban birin karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna.
Harin ya auku bayan sa'o'i kadan da miyagun 'yan bindiga suka kutsa asibiti tare da sace ma'aikatan jinya da jarirai a jihar Kaduna.
A wani labari na daban, mayakan ISWAP wadanda ba a san yawansu ba sun sheka lahira bayan arangamar da suka yi da jami'an tsaron hadin guiwa a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno.
'Yan ta'addan wadanda aka gani cikin kayan sojoji sun kai farmaki tare da budewa wata tawagar jami'an 'yan sanda wuta a yammacin Juma'a yayin da suke dawowa daga Buni Yadi kusa da Auno-Garin Kuturu a karamar hukumar Kaga.
An gano cewa 'yan ta'addan sun kwace wata mota daya da take mallakin jami'an tsaron, TheCable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng