Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar jihar Kano ta dakatar da Muhyi Magaji

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar jihar Kano ta dakatar da Muhyi Magaji

  • An dakatar da shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta Jihar Muhyi Magaji Rimin Gado
  • Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Muhyi ne saboda kin amincewa da akawun da aka tura masa daga ofishin babban akawun jihar Kano
  • Hakan na zuwa ne bayan ofishin babban akawun ta shigar wa majalisar dokokin jihar korafi game da Muhyi saboda nada wani ma'aikaci mai mataki na 4 matsayin akawu

Rahoton da BBC ta wallafa na cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Muhyi Magaji Rimin Gado, shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da cin hanci da rashawa na jihar na tsawon wata daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa dakatarwar na Muhyi na zuwa ne sakamakon kin amincewa da ya yi da akawun da aka aika masa daga ofishin babban akawun jihar Kano.

Muhyi Magaji
Muhyi Magaji Rimin Gado, shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano. Hoto: Daily Trust

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Hakan ya biyo bayan korafin da ofishin babban akawun jihar ya shigar ne a gaban majalisar dokokin jihar a kan Muhyi.

Muhyi na nada wani ma'aikaci da ke mataki na hudu a matsayin akawun hukumar wanda hakan ya sabawa tanadin doka kamar yadda wata wasika ta nuna.

Alhaji Labaran Madari, shugaban masu rinjaye na majalisar Kano ya bukaci kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar ya cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

KU KARANTA: El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba

Hakazalika, ya kuma nemi kwamitin da ya mika rahotonsa gaban majalisa nan da makonni biyu masu zuwa.

Mambobin kwamitin binciken

Shugaban kwamitin sauraron korafin jama'a na majalisar, Hon Umar Musa Gama ne zai jagoranci binciken sannan ya mika rahoton cikin wa'adin da aka diba wa kwamitin na sati biyu.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Hon Lawan Shehu shugaban kwamitin shari'a na majalisa, Shugaban kwamitin kudi Hon Dahiru Zarewa, Hon Sale Ahmad Marke shugaban kwamitin Aikin Hajji da Hon Salisu Ibrahim Doguwa shugaban kwamitin kula da hada-hadan kudaden gwamnati.

A makon da ta gabata, dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawar ya ce ofishin babban akawun jihar bata da ikon nada wa hukumarsa akawu a doka.

Rashin jituwar nan ta samo asali ne bayan hukumar ta fara bincike kan wasu kwangiloli da aka ce sun shafi wasu iyalan gidan gwamna.

Amaechi ya sanar da ranar fara aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano da zai laƙume $1.2bn

A wani labarin, Rotimi Amaechi, ministan sufuri na Nigeria ya ce za a fara aikin shimfida layin dogo na Kaduna zuwa Kaduna da zai lashe Dalla Biliyan 1.2 nan da makonni biyu, The Cable ta ruwaito.

Amaechi ya bada wannan sanarwar ne yayin wata taron manema labarai da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a ranar Juma'a a Abuja.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta amince da aikin na layin dogo daga Kaduna zuwa Kano ne a Janairun shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164