Iyaye sun fusata kan dalilin El-Rufai na cire dan shi daga makarantar gwamnati

Iyaye sun fusata kan dalilin El-Rufai na cire dan shi daga makarantar gwamnati

  • Iyayen dalibai sun nuna rashin jin dadinsu kan dalilin da yasa Gwamna Nasir ya cire dan shi daga Kaduna Capital School
  • A cewar wani mahaifin dalibai a makarantar, gwamnan ya ci amanarsu da bai sanar dasu halin tsaron da ake ciki ba
  • Wata mahaifiyar dalibai kuwa cewa tayi gwamnan yayi daidai da ya cire dan shi saboda zai kasance matsala ga yaransu

Wasu daga cikin iyayen yaran Kaduna Capital School dake yankin Malali sun yi martani ga Gwamna Nasir el-Rufai kan dalilansa na cire dan sa daga makarantar inda suka ce gwamnan yayi kuskure da bai sanar da makarantar da iyayen dalibai kalubalen tsaro da ake fuskanta ba.

A shekarar da ta gabata ne gwamnan ya saka dan shi a daya daga cikin tsoffin makarantun gwamnati ta Najeriya.

KU KARANTA: Luguden wuta yaran Igboho suka fara mana da muka je bincike, DSS

Iyaye sun fusata kan dalilin El-Rufai na cire dan shi daga makarantar gwamnati
Iyaye sun fusata kan dalilin El-Rufai na cire dan shi daga makarantar gwamnati. Hoto daga dailytrust
Asali: UGC

KU KARANTA: Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari

Daily Trust ta ruwaito yadda El-Rufai cikin sirri ya cire dan sa daga makarantar.

Muyiwa Adekeye, mai bada shawara na musamman ga gwamnan kan yada labarai yayi shiru duk da an bukaci sanin dalilin cire yaron daga makarantar.

Amma kuma a wata tattaunawa da gwamnan yayi da BBC Pidgin bayan wallafar, El-Rufai ya ce 'yan bindiga suna ta fakon dan shi saboda matsayarsa na hana kudin fansa.

El-Rufai ya ce wannan ne karo na farko da ya fara magana kan lamarin, ya kara da cewa diyarsa Nesrin an saka ta makarantar bayan ta cika shekaru shida.

Ya ce duk da babu wata barazana a kan Nesrin, ya cire dukkan yaran daga makarantar saboda hukumomin tsaro sun shawarci hakan.

A yayin martani ga tattaunawar, Alhaji Badamasi Ibrahim, wanda yaranshi ke makarantar, ya ce bashi da wani zabi da ya wuce ya cire yaranshi daga makarantar ko kuma su dakata da zuwa ganin cewa ana kokarin kai farmaki.

Wata mahaifiyar dalibai wacce ta bukaci a adana sunanta ta jinjinawa kokarin El-Rufai inda yace zaman dan sa a makarantar ne zai zama matsala ga sauran yara.

Ta ce, "Cigaba da zaman yaron ne zai cigaba da kawo barazanar, don haka nake tunanin ya yi abinda ya dace. A gaskiya za a dinga kashe kudi wurin baiwa yaro daya kariya idan aka cigaba da barin shi a makarantar."

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Borno na shirin sake gina garin Malam-Fatori wanda jama'ar garin suka bar shi wurin shekaru bakwai da suka gabata bayan harin 'yan ta'addan Boko Haram.

Da yawa daga cikin mazauna garin sun garzaya Bosso da Diffa ta jamhuriyar Nijar domin neman mafaka tun a shekarar 2014.

Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar Juma'a ya ziyarci garin Malam-Fatori, hedkwatar karamar hukumar Abadam wacce ke yankin tafkin Chadi na arewacin Borno.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel