Bidiyon saurayin da ya baiwa budurwa kyautar N2.5m saboda ta amince zata aure shi
- Wata budurwa 'yar Najeriya ta sha mamakin rayuwarta bayan ta amince da tayin auren da saurayinta yayi mata
- A wani bidiyo da ya janyo maganganu, an baiwa budurwar N2.5 miliyan daga saurayinta saboda ta amince za ta aure shi
- Kafafen sada zumunta sun yi martani kan bidiyon inda suka dinga mamakin irin kyautar girman da saurayin yayi mata
Wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita kafafen sada zumunta bayan ta amince da tayin auren saurayinta.
Matar mai amfani da @swiss_scarlet a Instagram, ta wallafa wani bidiyo inda saurayinta ya gwangwajeta da N2.5 miliyan saboda ta amince da tayin aurensa.
KU KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun sheke direba, sun sace mai ciki da mutum 32 a Kachia
KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana sabon salon FG na kawo karshen 'yan bindiga da masu satar mutane
Kamar yadda Instabog9ja ta tabbatar, budurwar masaniya ce a fannin hada mayuka. A wani bidiyo dake yawo, an boye fuskar saurayin sai dai hannunsa kadai ake iya gani inda yake zuba mata ruwan lemu a kofi tare da saka mata zobe a hannu.
Budurwar cike da jin dadi tare da annashuwa ta nuna mamakinta game da dunkulin kudin da aka bata.
Martani kala-kala sun biyo baya
Mutane da yawa sun ji dadin abinda saurayin yayi yayin da wasu suka ce duk buge ne, zai amshe kudinsa bayan an gama bidiyon.
@sharon_keduka cewa tayi: "Ina jin dadin yadda bana damuwa da abubuwa irin haka... Bana miki bakin ciki, kuma bana farinciki. Gani nan dai."
@kingsose.1 ya rubuta: "A Najeriya ne kadai ake haka. Ka baiwa yarinya makuden kudi saboda ta amince za ta aureka. A kan mene? Me ya faru??"
@africanflamingo_ yayi tsokaci da: "Wadannan mutanen basu gajiya da karya. Suna mantawa cewa jama'a sun san su."
@stoners_kingdom martani yayi da: "Bai ma yi kama da mutumin dake da miliyan 2 a asusun bankinsa ba."
A wani labari na daban, shugabar kwalejin koyar da jinya tare da ungwan zoma, Rukaiya Shettima Mustapha ta samu takardar tuhuma a kan dakatar da wasu dalibai da tayi kan cewa basu bi ayari sun fita tarar shugaba Buhari ba.
Legit.ng ta tattaro cewa Juliana Bitrus, wacce ita ce kwamishinan lafiya ta jihar ta aike da wasikar tuhumar inda take bukatar karin bayani kan lamarin cikin sa'o'i 48.
Wannan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng