Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda

Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda

  • Hankula sun fara tashi yayin da rikici ya fara kamari a yankin Ojota na jihar Legas
  • An gano cewa masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa sun bijirewa umarnin 'yan sanda
  • Tuni jama'a suka fara gudun ceton ransu yayin da 'yan sanda ke watsa barkonon tsohuwa da kama wasu

Rikici ya rincabe a yankin Ojota na jihar Legas yayin da masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa suka bijirewa umarnin 'yan sanda suka fara zanga-zanga.

Duk da 'yan sanda da sojoji sun mamaye wurin zanga-zangar a sa'o'in farko na yau Asabar, masu zanga-zangar daga bisani sun tsinkayi wurin, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Jerin sunaye: Jihohin APC da na PDP bayan sauya shekar Matawalle

Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda
Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama

Amma kuma jami'an tsaro dauke da bindigogi sun yi kokarin hana su zanga-zangar.

Hakan ya janyo barazana ga zaman lafiyan yankin yayin da jama'a suka fara gudun ceton rai kuma 'yan sanda suka dinga watsa barkonon tsohuwa.

'Yan kasuwa masu tarin yawa sun rufe shagunansu domin gudun su fada lamarin kuma su tafka muguwar asara.

Kamar yadda Daily Trust ta gani, wasu 'yan sanda sun fara kama wasu daga cikin masu zang-zangar.

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, jami'an tsaro na farin kaya sun yi ikirarin cewa wasu maza da suke tsammanin masu tsaron Sunday Igboho ne sun yi musayar wuta da jami'ai a yayin samamen da suka kai gidan mai assasa samar da kasar Yarabawa a Ibadan da safiyar Alhamis.

Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis bayan kama mutum 13 a gidan Igboho, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda Afunanya ya sanar, samamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu na cewa ana tara makamai a gidan Igboho, lamarin da yasa ake samun rashin zaman lafiya a yankin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel