Zulum zai sake gina garin Malam-Fatori bayan barinsa da aka yi na shekaru 7
- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno zai sake gina garin Malam-Fatori dake Abadam
- Yanzu haka shekarun garin bakwai babu mutane tun bayan addabarsu da Boko Haram tayi
- Gwamna Zulum ya shiga garin inda ya dudduba tare da ganawa da sojojin dake cikin garin
Gwamnatin jihar Borno na shirin sake gina garin Malam-Fatori wanda jama'ar garin suka bar shi wurin shekaru bakwai da suka gabata bayan harin 'yan ta'addan Boko Haram.
Da yawa daga cikin mazauna garin sun garzaya Bosso da Diffa ta jamhuriyar Nijar domin neman mafaka tun a shekarar 2014.
KU KARANTA: Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama
KU KARANTA: Bidiyon Hanan Buhari cikin taron Turawa ta garzaya karbar kwalin digirinta na 2
Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar Juma'a ya ziyarci garin Malam-Fatori, hedkwatar karamar hukumar Abadam wacce ke yankin tafkin Chadi na arewacin Borno.
A wata takarda da mai bada shawara ga gwamnan na musamman, Malam Isa Gusau ya fitar a Facebook, ya ce sun kai ziyarar ne domin fara duba yadda za a gyara wurin kuma 'yan gudun hijira su dawo daga Bosso da Diffa a jamhuriyar Nijar.
Zulum ya amince da bada motocin sintiri 10 domin inganta tsaro kuma ya tattauna da babban kwamandan bataliya ta 68 dake Malam-Fatori domin gano wuraren da gwamnatin jihar Borno za ta bada tallafi.
A yayin jawabi ga dakarun, Zulum ya jinjinawa kokarin dakarun tare da basu kwarin guiwa kan su cigaba da kokari wurin kawar da ragowar 'yan ta'adda dake kusa da Malam-Fatori.
Gwamnan daga bisani ya duba abubuwan more rayuwa da 'yan ta'addan suka lalata a garin wanda yace za a gyara su kafin watan Disamba.
Zulum ya je Malam-Fatori bayan ya ziyarci garin Diffa a ranar Alhamis, inda ya samu tattaunawa da shugaban kasa Bazoum Mohammed na jamhuriyar Nijar.
A wani labari na daban, an shiga tashin hankali a sakateriyar jam'iyyar APC a ranar Alhamis a garin Abuja bayan an dinga rade-radin cewa ginin zai rushe.
Sakateriyar APC ta kasa tana nan a lamba 40, titin Blantyre dake Wuse 11, Abuja, babban birnin tarayya, Daily Trust ta ruwaito.
Wani ganau ba jiyau ba wanda ya zanta da manema labarai, ya ce daya daga cikin ma'aikatan dake bene hawa na hudu ya koka da yadda ginin ke rawa.
Asali: Legit.ng