Sunday Igboho Ya Tura Sako Ga FG, Yana Neman Diyyar Makudan Kudade
- Sunday Igboho ya nemi gwamnatin tarayya ta biya shi diyyar barnar da jami'an tsaro suka yi masa
- Ya bayyana cewa, an tafka masa a gidansa lokacin da jami'an tsaro suka je domin bincike da kame wasu
- A baya an kame matarsa da wasu mutane a cikin gidan nasa gabanin fara gangamin kafa kasar Yarbawa
Sunday Igboho a ranar Asabar ya rubuta takardar koke ga gwamnatin tarayya kan barnar da aka yi wa gidansa, motoci da sauran kadarori da jami'an tsaro suka yi, The Nation ta ruwaito.
Ya yi kiyasin asarar da ya yi cewa ya kai Naira miliyan 500 kuma ya nemi a biyashi wannan kiyasi.
Igboho, a cikin wata wasika ta hannun mai ba shi shawara Cif Yomi Alliyu (SAN) ya kuma nemi gafara daga jama'a kan abin da ya kira take hakkinsa da aka yi a lokacin da aka mamaye gidansa da kuma wani binciken da jami'an tsaro suka yi.
KARANTA WANNAN: NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta
Lauyan ya yi zargin cewa wadanda aka kama a gidan Igboho ana azabtar da su don su amsa cewa an gano bindigogi da alburusai daga gidansa.
An Yi Awon Gaba da Matar Sunday Igboho Bayan Kame Nnamdi Kanu
Matar mai fafutukar kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ta shiga hannun ‘yan bindiga da suka kai hari gidansa da safiyar ranar Alhamis.
Wannan na zuwa ne kamar yadda shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin cin gashin kai na Yarbawa, Ilana Omo Oodua, Emeritus Farfesa Banji Akintoye ya fada.
Ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma Manajan Sadarwar kungiyar, Mista Maxwell Adeleye ya gabatar wa manema labarai, Punch ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: 'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace
An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe
A wani labarin daban, Jihar Legas - A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo, rundunar 'yan sanda ta jihar ta cafke wasu daga cikin masu gangamin kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa a yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a jiya Asabar a cikin jihar.
Bayan tabbatar da kamun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu ya gabatar da wasu mutane 47 da aka kama a wurin zanga-zangar ta nuna goyon baya ga kafa haramtacciyar kasar Yarbawa.
An gabatar da hotuna, mazuban abinci, layu, da sauransu a matsayin abubuwan da aka kame yayin zanga-zangar.
Asali: Legit.ng