Bayan Kame Nnamdi Kanu, Yarbawa Sun Gargadi Sunday Igboho Kan Fafutukar Ballewa

Bayan Kame Nnamdi Kanu, Yarbawa Sun Gargadi Sunday Igboho Kan Fafutukar Ballewa

  • Kungiyar Yarbawa ta shawarci Sunday Igboho kan dagewa da yake yi na ballewa daga Najeriya
  • Kungiyar ta ce ya kamata Sunday Igboho ya koyi darasi daga abinda ya faru da Nnamdi Kanu takwaransa
  • Bayan kame Nnamdi Kanu, an kai hari gidan Sunday Igboho, inda aka sace matarsa da wasu mutane da dama

An aika sako ga mai rajin ballewar Yarbawa daga Najeriya, Sunday Adeyemo Igboho da aka fi sani da Sunday Igboho.

Sakon wanda Kungiyar Walwalar Yarbawa (YWG) ce ta aiko dashi, in ji jaridar Daily Trust, shi ne: - ya dauki darasi daga abinda ya faru da Nnamdi Kanu.

Wannan na zuwa ne yayin da Igboho ke dagewa kan cewa babu gudu babu ja da baya a ranar Asabar, 3 ga watan Yuli cewa sai ya gudanar da taron Yarbawa a jihar Legas.

KARANTA WANNAN: Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

Yarbawa Sun Gargadi Sunday Igboho, Sun Ce Ya Dauki Darasi Daga Nnamdi Kanu
Mai rajin kafa kasar Oduduwa ta Yarbawa | Hoto: centapost.com
Asali: UGC

Shugaban kungiyar, Kwamared Abdulhakeem Alawuje ya shawarci Igboho da kada ya tsunduma kansa cikin ayyukan da za su jefa yankin kudu maso yamma cikin rikici kamar yadda ake gani a yankin kudu maso gabas.

Ya ce:

“Tare da duk goyon bayan da Kanu ya yi ikirarin yana da shi, an kama shi kamar kaza kuma an dawo da shi Najeriya ba tare da wata hayaniya ba. A yanzu da muke magana, ana ci gaba da shari’arsa a babbar kotun Abuja.”

An Yi Awon Gaba da Matar Sunday Igboho Bayan Kame Nnamdi Kanu

Matar mai fafutukar kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ta shiga hannun ‘yan bindiga da suka kai hari gidansa da safiyar ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne kamar yadda shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin cin gashin kai na Yarbawa, Ilana Omo Oodua, Emeritus Farfesa Banji Akintoye ya fada.

Ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma Manajan Sadarwar kungiyar, Mista Maxwell Adeleye ya gabatar wa manema labarai, Punch ta ruwaito.

Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

Kungiyar 'World Igbo Congress' ta bukaci Gwamnatin Burtaniya da ta kare hakkokin jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, bayan kamun da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi masa.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Kanu dan kasar Birtaniyya ne, don haka, ya kamata gwamnatin Burtaniya ta kiyaye masa hakkinsa a matsayin dan kasa, Punch ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Anthony Ejiofor da kuma Jami’in Hulda da Jama’a, Basil Onwukwe ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Jawabin World Igbo Congress game da kame Mazi Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi’.

KARANTA WANNAN: Yadda PDP Ta Mulki Jihohi 31 Shekaru 14 da Suka Gabata da Yadda APC ta Kwacesu

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Yadda Nnamdi Kanu Ya Kashe Mutane Sama da 60

A wani labarin, Gwamnatin Najeriya ta zargi shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da kitsa kisan mutane sama da 60 cikin watanni hudu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yi wannan zargin ne cikin wata wasika da ta aike wa jami’an diflomasiyyar kasashen yamma.

Wasikar wacce ke dauke da kwanan watan 26 ga watan Afrilu, 2021, ta yi zargin cewa Kanu ne ke da alhakin lalata kadarori a wasu hare-hare 55 da suka auku a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.