Jami'an hukumar Amotekun sun damke Shanun Fulani sama da 400
- Rundunar Amotekun ta bayyana nasarar kame shanu fiye da 400 tare da kakkabe bata-gari da dama a Akure babban birnin jihar
- Kwamandan rundunar ya bayyana cewa ana samun nasarar aiki tsakanin jami’an Amotekun da sauran takwarorinta
- A cikin makon nan rundunar za ta rarraba sababbin jami’anta guda 500 zuwa kananan hukumomin jihar
Rundunar tsaro ta Amotekun a Jihar Ondo ta ce ta jami’anta sun kame akalla shanu 400 a wani sintirin da ta kira ‘Samamen Shara’ da take gudanarwa a jihar.
Kwamandan rundunar a jihar, Chif Adetunji Adeleye, shi ya sanar da haka yayin da yake ganawa da manema labarai a Akure babban birnin jihar, rahoton Punch
Ya kuma bayyana cewa umarnin da gwamnatin jihar ta bai wa dukkanin kananan hukumomin jihar da su kafa jami’an ‘yan banga kwalliya na biyan kudin sabulu.
DUBA NAN: Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa
KU KARANTA: Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki
Ya ce,
“Mun fara ne daga babban birnin jiha inda muka toshe dukkanin kofofin barna tare da kame shanu fiye da 400 kafin daga bisani muka fantsama kananan hukumomin da ke Arewacin jihar inda muke sintirin sa’o’i 24.
“Muna aiki tare da ‘yan banga da mafarautan yankunan a sintirin dazukan da muke yi. Mun yi nasarar kakkabe ‘yan iska a kwanakin nan. Hakan ya sanya kuke jin galibin sace mutane da ake yi a yanzu suna faruwa ne a kan iyakokinmu.
“Karamar Hukumar Ose tana iyaka da Jihar Kogi kuma tana bada damar zullewa cikin sauki. Amma muna nan muna ta bibiyar su.”
Ya ce nan ba da jimawa ba rundunar za ta rarraba sababbin jami’anta guda 500 da ta dauka aiki zuwa wuraren da za su aiki cikin fadin jihar.
Muna bukatan makamai, Amotekun
A bangare guda, kwamandan rundunar tsaro ta Amotekun a Jihar Ekiti, Joe Komolafe, ya bayyana haramta wa rundunar Amotekun daukar makamai da aka yi, a matsayin babban abin da ya haifar da koma baya a yaki da 'yan fashi da sauran matsalolin tsaro a yankin Kudu maso Yamma.
Mista Komolafe, wanda Birgediya Janar mai ritaya ne, ya fadi hakan a ranar Litinin lokacin da yake bayani a wani shirin gidan rediyon Crest FM, da ke Akure.
Asali: Legit.ng