Dalilin da ya sa ba mu murkushe ’yan bindiga ba - Kwamandan Amotekun
- Kwamandan Amotekun ya koka cewar rashin bai wa jami’an Amotekun manyan makamai na takaita karfin rundunar
- Sai dai ya ce duk da rashin mallakar makaman rundunar tana iya bakin kokarinta wajen yakar miyagu
- Sannan ya ce Amotekun din ta himmatu wajen ci gaba da kare jihohin Kudu maso Yamma
Kwamandan rundunar tsaro ta Amotekun a Jihar Ekiti, Joe Komolafe, ya bayyana haramta wa rundunar Amotekun daukar makamai da aka yi, a matsayin babban abin da ya haifar da koma baya a yaki da 'yan fashi da sauran matsalolin tsaro a yankin Kudu maso Yamma.
Mista Komolafe, wanda Birgediya Janar mai ritaya ne, ya fadi hakan a ranar Litinin lokacin da yake bayani a wani shirin gidan rediyon Crest FM, da ke Akure.
Ya ce, duk da cewa rundunar ta samu gagarumar nasara wajen magance matsalar tsaro da 'yan ta'adda a yankin, amma da aikin rundunar zai fi kyau idan aka bar rundunar ta mallaki manyan makamai.
A cewarsa, babu wata doka a cikin dokar da ta kafa rundunar tsaron da ta bayar da damar daukar nau'ukan makamai kamar bindigogin AK47 da sauran manyan makamai masu sarrafa kansu.
Ya ce lamarin na da matukar wahala wajen tunkarar 'yan ta'addan da ke dauke da muggan makamai.
Yace:
" 'Yan sanda ne kawai aka ba su ikon daukar irin wadannan makamai sannan idan muka kama wadanda ake zargin za mu mika su ga 'yan sanda don gurfanar da su,."
"Amma duk da cewa ba mu da makamai, lokacin da miyagun suka gan mu sai su gudu, saboda muna da hanyar da za mu bi da irin wannan yanayin kuma sun san mu, don haka da zarar mun bayyana sai su ranta a na kare."
KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997
KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997
Sai dai ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da aikinta na kiyaye jihohi da yankin duk kuwa da rashin ba ta damar rike manyan makaman ba.
An sanya mafarautan yankin cikin dakarun rundunar tsaron wadanda galibi suke dauke da bindigogin harba ka labe da wasu makamai kirar gida.
Matsalar tsaro ta game Najeriya
Jihar ta Ekiti tana fama da kalubalen tsaro iri-iri kama daga na rikice-rikice da sace-sace da na 'yan fashi a cikin 'yan kwanakin nan, inda mutane da dama suka rasa rayukansu a cikin lamarin.
Wadanda suka tsira daga irin wadannan hare-hare sun samu yancin nasu ne bayan an biya kudaden fansa ga wadanda suka sace su.
A fara baiwa Amotekun AK-47
Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce idan doka ta yarda, zai gwammace jami'an bangan Amotekun, su dauki bindigogin AK-47 don bunkasa ayyukan tsaro.
Gwamnan ya fadi haka ne a jawabin da ya gabatar a garin Ibadan ranar Talata a wajen bude taron dimokiradiyya na kasa mai taken, "Makomar dimokuradiyya a Najeriya."
Asali: Legit.ng