Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki

Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki

  • Shugaban kamfanin Total Grace Oil and Gas, Dr Henry Bolaji Akinduro, ya ce da N50,000 ya fara kasuwanci
  • A cewarsa, kudin da gwamnatin jihar Ondo ta bashi matsayin dan makaranta ya fara kasuwancin da su
  • Yace abin dai ba sauki amma sai mutum ya dage kuma ya kara da hakuri

Dr Henry Bolaji Akinduro, shugaban kamfanin Total Grace Oil and Gas Investment Limited, ya bayyana cewa dukiyar da ake ganin yana da su yanzu, da jarin N50,000 ya fara.

Kamfaninsa na da hedkwata a Dubai, kuma yana da gidajen mai biyar a Najeriya.

A hirar da yayi da Legit.ng, attajirin ya yi bayanin cewa N50,000 da ya samu matsayin kudin tallafin da gwamnatin jihar Ondo ta bashi yana karatun likitanci a jami'a yayi amfani da su.

Da aikin Fotocofi ya fara

Dr Akinduro, a ranar Laraba, ya kara da cewa da aikin komfuta da fotokofi ya fara.

Yace:

"Na kwana biyu ina gwagwarmaya. Na fara da N50,000 da gwamnatin Ondo ta bani lokacin da nike karatun Likitanci matsayin tallafi.
"Daga nan, muka bude shago da fotokofi da komfuta.
"Bayan shekaru biyu, dirakta na ya shigo harkar. Daga nan, muka fara kasuwanci daban-daban."

Da jarin N50,000 na fara kasuwanc
Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki Hoto: Dr Bolaji Akinduro
Asali: UGC

Babu sauki dai

Attajirin ya bayyana cewa abin dai ba sauki saboda ya fuskanci kalubale daban-daban amma ire-iren wadannan kalubalen ne suka karfafashi.

Saboda haka, Akinduro, ya yi kira da yan kasuwa masu tasowa su rungumi hakuri saboda ba zasu iya arziki a dare daya ba.

"Abin ba sauki. Kowani kasuwa na da kalubale. Amma iya dakile kalubalen ne zai karfafa ka," yace

Asali: Legit.ng

Online view pixel