Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa
- Kotu ta zabi ranar yanke hukunci kan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky
- Gwamnatin Kaduna ta shigar da Zakzaky da iyalinsa kotu
- An tsare Zakzaky tun Disamban 2015
Babbar kotu a jihar Kaduna ta zabi ranar Alhamis, 28 ga Yuli, domin yanke hukunci kan shugaban mungiyar mabiya akidar Shi'a, Ibrahim Zakzaky, da uwargidarsa, Zeenat.
Alkali Gideon Kurada ya zabi ranar ne bayan lauyoyin Zakzaky da na Gwamnati suka tattauna da kotu kan bukatar watsi da karar da aka shigar kan Zakzaky.
Kamfanin dillancin labarai NAN ta rahoto Lauyan Zakzaky, Femi Falana, wanda yayi hira da manema labarai bayan zaman kotun ya bukaci kotun ta baiwa Zakzaky nasara.
Yace:
"Lauyoyin masu kara da masu kare wanda ake zargi sun yi wa kotu jawabi kan bukatar soke karar."
"A baya mun bayyana cewa duk da lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidu 15, muna ganin babu wani kwakkwarin hujjan shigar da mutuminmu (Zakzaky) kotu."
"Kotu ta saurare mu kuma an zabi ranar 28 ga Yuli don yanke hukunci kan hakan.
Lauyan Gwamnati, Dari Bayero, ya ce sun bukaci kotu ta yankewa Zakzaky da Matarsa hukuncin dauri a gidajen yari.
Gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi El-Zakzaky da Zeenat da laifuka takwas, wanda suka hada da kisan kai, tayar da tarzoma, dss.
Zakzaky da Matarsa sun ce karya akayi musu.
Asali: Legit.ng