Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Yadda Nnamdi Kanu Ya Kashe Mutane Sama da 60

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Yadda Nnamdi Kanu Ya Kashe Mutane Sama da 60

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda shugaban haramtacciyar ta'addanci ta IPOB ya hallaka mutane 60 cikin watanni hudu
  • Gwamnati ta ce Nnamdi Kanu na ba da umarnin aikata ta'addanci ne a maboyarsa ta Landan
  • Ta zarge shi da amfani da gidan Rediyon Biafra wajen kitsa dukkan munanan hare-haren da suka faru sama da 50

Gwamnatin Najeriya ta zargi shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da kitsa kisan mutane sama da 60 cikin watanni hudu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yi wannan zargin ne cikin wata wasika da ta aike wa jami’an diflomasiyyar kasashen yamma.

Wasikar wacce ke dauke da kwanan watan 26 ga watan Afrilu, 2021, ta yi zargin cewa Kanu ne ke da alhakin lalata kadarori a wasu hare-hare 55 da suka auku a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu.

KARANTA WANNAN: An Bindige Wani Dalibin Jami’a Bayan Rubuta Jarrabawarsa Ta Karshe a Jami’a

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Yadda Nnamdi Kanu Ya Kashe Mutane Sama da 60
Shugaban Kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

FG tace Kanu ya shirya hare-haren ne daga sansanin sa na Landan

Ma’aikatar harkokin kasashen waje a cikin wasikar ta zargi shugaban na IPOB da bayar da umarni ga ‘yan kungiyarsa ta ESN, inda suka kai munanan hare-hare a cikin yankunan biyu a Najeriya.

Wasikar ta ce:

”A cikin kasa da watanni hudu a wannan shekarar, IPOB ta aikata munanan ayyuka hamsin da biyar (55) a sassa daban-daban na Kudu maso Gabashin Najeriya inda suka kashe mutane da dama tare da lalata kadarori da dama.
"Tabbas zai zama kamar matsayin (kasashen yamma) ya kara karfafa gwiwar Nnamdi Kanu dake ikirarin shugabancin IPOB."

A cewar jaridar Premium Times, gwamnatin ta yi zargin cewa umarnin da Kanu ya bayar ya fito ne daga sansaninsa da ke Landan ta hanyar amfani da gidan Rediyon Biafra.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mambobin haramtacciyar kungiyar sun addabi cibiyoyin tsaro da wasu cibiyoyin gwamnati a dukkan yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu.

KARANTA WANNAN: Ni Ba Mai Cin Hanci da Rashawa Bane, Kowa Ya Sani, Buhari ya Jaddada Martabarsa

Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

A wani labarin, Kungiyar 'World Igbo Congress' ta bukaci Gwamnatin Burtaniya da ta kare hakkokin jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, bayan kamun da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi masa.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Kanu dan kasar Birtaniyya ne, don haka, ya kamata gwamnatin Burtaniya ta kiyaye masa hakkinsa a matsayin dan kasa, Punch ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Anthony Ejiofor da kuma Jami’in Hulda da Jama’a, Basil Onwukwe ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Jawabin World Igbo Congress game da kame Mazi Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi’.

Asali: Legit.ng

Online view pixel