Wasu Mutum 11 Sun Lakaɗawa Wata Mata Dukan Tsiya Har Ta Mutu a Gidan Sarkin Kano

Wasu Mutum 11 Sun Lakaɗawa Wata Mata Dukan Tsiya Har Ta Mutu a Gidan Sarkin Kano

  • Yan sanda a jihar Kano, sun yi ram da wasu mutum 11 da ake zargin suna da hannu a kashe wata mata
  • Mutanen sun lakaɗawa matar dukan tsiya har ta mutu bisa zargin cewa matar mayya ce
  • Kakakin yan sanda a Kano, DSP Kiyawa, yace a halin yanzun suna cigaba da bincike domin gano sauran mutanen

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta cafke wasu mutum 11 da take zargin suna da hannu a dukan kawo wuƙa da aka yiwa wata mata wanda yayi sanadiyyar mutuwarta bisa zargin maita a gidan sarkin Kano.

KARANATA ANAN: Da Ɗuminsa: Gwamna Zulum Ya Shilla Ƙasar Nijar, Ya Sa Labule da Shugaba Bazoum

Rundunar ta bayyana cewa ta samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne ranar Talata, kuma ta na cigaba da bincike don kamo sauran.

Kakakin yan sanda a jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC hausa cewa lamarin ya faru ne tun ranar Asabar da ta gabata, kuma an yi jana'izar matar kamar yadda addinin musulunci ya tanazar.

Dogarawa 11 Sun Lakaɗawa Wata Mata Dukan Tsiya Har Ta Mutu
Wasu Mutum 11 Sun Lakaɗawa Wata Mata Dukan Tsiya Har Ta Mutu a Gidan Sarkin Kano Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin dogarawan Sarkin Kano ne suka aikata wannan ɗanyen aiki bisa zargin matar ta kama wata yarinya dake ɓangaren matan marigayi Ado Bayero.

A jawabin DSP Kiyawa, yace: ""Mun fara samun labarin ne ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata. Binciken mu ya nuna tun ranar Asabar abin ya faru."

"Kuma lokacin da batun ya zo mana ma har an binne matar. Mu kuma muka ga akwai buƙatar bincike. Har yanzu muna gudanar da binciken amma ba mu kammala ba."

"Da farko mun fara samun mutum biyu, daga baya muka sake samun mutum tara, maza shida mata uku. Akwai wadanda muke nema kuma insha Allah za mu kama su."

KARANTA ANAN: Wasu Fusatattun Mata da Ƙananan Yara Sun Toshe Hanyar Sokoto-Gusau

Yan Sanda ba su bayyana sunan matar da aka kashe ba

Rundunar yan sanda a Kano bata bayyana ainihin sunan matar da lamarin ya shafa ba, amma a wani bincike da BBC ta gudanar ta gano cewa matar yar asalin ƙaramar hukumar Warawa ce.

Da aka tuntuɓi shugaban ma'aikatan fadar sarkin Kano, Alhaji Ahmad Ado Bayero, bai msa waya ba.

A wani labarin kuma Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

IGP Usman Baba, ya bayyana wa yan majalisar wakilai cewa hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin bada tsaro ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan hukumar yan sanda ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel