An Bindige Wani Dalibin Jami’a Bayan Rubuta Jarrabawarsa Ta Karshe a Jami’a

An Bindige Wani Dalibin Jami’a Bayan Rubuta Jarrabawarsa Ta Karshe a Jami’a

  • Wasu 'yan bindiga sun hallaka dalibin jami'a a jihar Benin bayan kammala jarrabawar karshe
  • Rahoto ya bayyana cewa, kashe dalibin na da alaka da kungiyoyin asiri da yankin ke fuskanta
  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa, tana kan bincike kan lamarin kuma za ta ba da bayani

Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani matashi dan aji hudu a sashen karatun kimiyyar siyasa a jami’ar Benin (UNIBEN) Austin Izu.

Izu, wanda kwanan nan ya zana jarabawarsa ta karshe, an kashe shi lokacin da ya ziyarci dakin abokinsa Walter Emeka, wani dakin kwanan dalibai da ke wajen makaranta a kan titin Kwalejin ’Yan Mata ta Tarayya dake Ugbowo.

Marigayin yana saukowa daga dakinsa ne a saman bene zuwa dakin abokinsa dake kasan ginin lokacin da lamarin ya faru.

KARANTA WANNAN: Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

An Bindige Wani Dalibin Jami’a Bayan Rubuta Jarrabawarsa Ta Karshe a Jami’a
'Yan bindiga rike da makamai | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

An ce wasu mutane hudu dauke da makamai kuma rufe da fuska sun shiga dakin suka kashe Izu a take yayin da aka harbi Emeka a hannunsa, lamarin da ya bar shi da mummunan rauni.

An ce Emeka na jinya a halin yanzu, yayin da aka ajiye gawar Izu a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin ta (UBTH).

Kontongs Bello, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Edo da ya tabbatar da faruwar lamarin ga TheCable Lifestyle a ranar Laraba, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

A cewar Bello, harin na da nasaba da rikici tsakanin kungiyoyin asiri a yankin, lura da cewa an cafke wanda ake zargi.

Bello yace:

"Eh, yana da alaka da kungiyar asiri, wani ya mutu a ranar Litinin, wani ya mutu a daren Talata yayin da daya kuma ya ji rauni a wannan ranar kuma a yanzu yana karbar magani a asibiti."

Lokacin da aka tuntube ta, Benedicta Ehanire, kakakin jami'ar ta Benin, ta ce tana wurin taro kuma ta yi alkawarin zantawa daga baya.

Bayan Harbe Mata Mai Juna Biyu da Sace Mijinta, 'Yan Bindiga Sun Nemi Fansar N3Om

'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta Wasu ‘yan bindiga, a ranar Asabar, sun harbe wata mata mai ciki har lahira tare da yin garkuwa da mijinta a karamar hukumar Offa da ke Jihar Kwara.

Marigayiyar, wacce wasu majiyoyi suka bayyana sunanta da Hawa, matar Lukman Ibrahim, wani dillalin wayar salula a Kasuwar Owode wanda aka fi sani da "LUKTECH", Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin, ya faru ne a daren Asabar 'yan mintoci kadan kafin karfe 7 na yamma yayin da Lukman ke tuka surukinsa, matarsa ​​mai juna biyu da yaronsu zuwa gida a kan hanyar Ojoku, kusa da Hedikwatar 'yan sanda.

KARANTA WANNAN: Najeriya Ta Hada Kai da Majalisar Dinkin Duniya Don Samarwa Kasa Abinci Mai Kyau

An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai ga ’Yan Bindiga

A wani labarin, Wani Sufeton ‘yan sanda, Nathaniel Manasseh, ya shiga hannun 'yan sanda a Jihar Kuros Riba bisa zargin dillancin bindigogi da alburusai ga masu aikata laifuka.

An cafke Manasseh a Calabar, babban birnin jihar, kuma aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda ranar Talata tare da sauran wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, an ce shi babban dillalin bindiga ne kuma ya dade yana wannan harkallar kafin dubunsa ya cika.

Sufeton da ya amsa laifin shi, an ce shi ne ke kula da ma'ajiyar makamai a rundunar 'yan sanda ta jihar kuma an kama shi ne lokacin da ya kasa ba da bahasin wasu kayan aiki ciki har da bindigogin AK-47 guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel