Hotunan iyalan Buhari da suka dira birnin London don yayen Hanan daga makaranta

Hotunan iyalan Buhari da suka dira birnin London don yayen Hanan daga makaranta

  • 'Ya'yan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun samu halarta yayen Hanan Buhari a London
  • Kamar yadda Aisha Buhari ta wallafa, Hanan ta kammala digirinta na biyu a fannin hoto
  • Ba iyalan Buhari kadai ba, mijin Hanan, Muhammad Turad tare da kannansa sun samu halarta

A kalla 'ya'yan shugaban kasa Muhammadu Buhari biyu ne suka halarci yayen diyar shugaban kasa, Hanan, daga Royal College of Art, London inda ta kammala digiri na biyu.

Hanan wacce ta kammala digiri na farko daga jami'a a Ingila a 2019, a cikin kwanakin nan ta kammala digirinta a bangaren hoto daga makarantar.

KU KARANTA: Dattijuwa mai shekaru 55 tayi haihuwar farko, mijinta ya tsere, ta samu kyautar N400K

Hotunan iyala Buhari da suka dira birnin London don yayen Hanan daga makaranta
Hotunan iyala Buhari da suka dira birnin London don yayen Hanan daga makaranta. Hoto daga @aishambuhari
Asali: Instagram

KU KARANTA: Karin kudin makaranta: Kaduna ta musanta amfani da jami'an tsaro wurin muzgunawa dalibai

Hanan Buhari ta auri Muhammad Turad Sha'aban a shekarar da ta gabata inda aka yi kayataccen biki.

Mijiinta ya halarci bikin yayen inda mahaifiyarta ta wallafa hotunansu tare da yi wa diyarta fatan alheri.

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, ya zagi jam'iyyarsa kan barazanar da take na maka Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a gaban kotu kan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC.

Fani-Kayode a jerin wallafar da ya dinga a shafinsa na Twitter, ya soki barazanar da ake wa Matawalle inda ya shawarci jam'iyyarsa da ta dage wurin janyo hankali, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Barazanar da PDP ke yi na kai Bello Matawalle kotu a kan komawa jam'iyyar APC ta rashin hankali ce."

Asali: Legit.ng

Online view pixel